Isra’ila ta zabi sabon shugaba

Majalisar dokokin kasar Isra’ila ta zabi Mista Reuben Riblin a matsayin shugaban kasa wanda  zai maye gurbin Shugaba Shimon Peres.Shekaranjiya Laraba ne majalisar ta kada kuri’ar zabensa, inda kuma ya samu kuri’u 63. Abokin takararsa kuma, Mista Meir Sheetrit ya samu kuri’u 53. Sabon  shugaban kasar wanda shi ne  tsohon shugaban majalisar kasar, dan jam’iyyar […]

Isra’ila ta zabi sabon shugaba
Isra’ila ta zabi sabon shugaba

Majalisar dokokin kasar Isra’ila ta zabi Mista Reuben Riblin a matsayin shugaban kasa wanda  zai maye gurbin Shugaba Shimon Peres.
Shekaranjiya Laraba ne majalisar ta kada kuri’ar zabensa, inda kuma ya samu kuri’u 63. Abokin takararsa kuma, Mista Meir Sheetrit ya samu kuri’u 53. Sabon  shugaban kasar wanda shi ne  tsohon shugaban majalisar kasar, dan jam’iyyar Likud ne, wadda Firaminista Benjamin Netanyahu ke jagoranta.
Da fari Mista Netanyahu ya yi dari-dari wajen ba shi goyon baya saboda wata takkadama da ta faru tsakaninsu a baya. Wannan ya sa Netanyahu ya yi ta jan kafa kafin a bayyana lokacin gudanar da zaben, a fatansa na ganin ya gabatar da wani dan takaran da zai samu nasara kan Mista Riblin.
Sabon shugaban mai shekara 74, yana da ra’ayin jari hujja ne kuma ba ya goyon bayan kafa kasar Palasdinu da janyewar Isra’ila daga Gabar Kogin Jordan. A maimakon wannan, ya na kira ne da a baiwa Palasdinawa takardar izinin zama a kasar Isra’ila.