Isra’ila za ta gane kurenta —Iran  

Ministan ya gargaɗi Isra’ila cewa ta kwana da sanin cewa makaman Iran za su iya isa duk inda aka harba su

Isra’ila za ta gane kurenta —Iran  

Ƙasar Iran ta gargaɗi Isra’ila cewa muddin ta kuskura ta yi gangancin kawo mata hari, to za ta yaba wa aya zaƙi. 

Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta yi wa Isra’ila jan kunnen ne da cewa kada ta kuskura ta kai haƙurinta bango

Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi, a cikin wata sanarwar, ya ce, “a yayin da Isra’ila ke gigin rama hare-haren da Iran ta kai mata a makon jiya, ta kwana da sanin cewa makaman Iran masu linzami za su iya isa duk inda aka harba su.

“Kuma mun riga mun shirya mu mayar da martani kan duk harin da aka kawo mana,” in ji Minista Araghchi.

Ya jaddada cewa Iran za ta ci gaba da goyon baya da kuma taimaka wa ƙungiyar Hamas da Hizbullah da duk wani yunƙurin ganin Palasɗinawa sun samu ƙasarsu mai cikekken ’yanci.

Da yake jawabi kan kisan shugaban Hizbullah, Sayyid Hassan Nasrallah da Isra’ila ta yi, ministan ya bayyana cewa fito-na-fito da Iran ke yi da Isara’ila ba kan mutum ɗaya ba ne kawai.

Lakurawa sun kashe ma’aikatan kamfanin Airtel 3 a Kebbi

Matashi ya kashe mahaifiyarsa don yin tsafi a Kuros Riba

DSS ta ceto mutum 4 da aka sace a Sakkwato

2025: Wutar lantarkin Najeriya ta ɗauke gaba ɗaya