ISWAP da Boko Haram sun kashe wa juna mayaka 41
Bangarorin biyu sun yi wa juna mummunar barna, inda mayakan da kwamnadojinsu suka sheka lahira a musayar wutar.
Kwamandoji da mayakan ISWASP da na Boko Haram 41 ne aka tabbatar sun mutu a wani kazamin fada tsakanin kungiyoyin ta’addancin a wani hari da ISWAP ta kai wa Boko Haram.
’Yan ta’addan sun ba hamata iska ne a yankin Duguri na Karamar Hukumar Kukawa na Jihar Borno, inda mayakan ISWAP da wani kwamandansu mai suna Bakura Buduma ya jagorance su suka far wa Boko Haram.
- Tinubu ya sake tura malaman Musulunci Nijar
- NAJERIYA A YAU: Shin Tinubu Zai Naɗa Ɗansa Ministan Matasa?
Tabbatattun majiyoyi sn ruwaito cewa bangarorin biyu sun yi wa juna barna, inda mayakan da kwamnadojinsu suka sheka lahira a musayar wutar.
Shi ma da yake tabbatar da hakan, Zagazola, kwararre kan abin da ya yaki da ta’addanci a yankin Tafkin Chadi, ya ce ISWAP ta fi yi wa Boko Haram barna, inda ta kashe kwamandojinta kusan goma a fadan.
Aminiya ta kawo rahoton yadda a kwanakin baya rikicin kabilanci a cikin kungiyar Boko Haram ya yi ajalin mayakanta da kwamandoji 82 lokaci guda.
Rahotanni sun nuna yanzu ISWAP ce ke samun galaba a kan Boko Haram bayan sauya sheka da wani babban kwamandanta Abou Idris ya yi daga Boko Haram.