ISWAP: Mun kawar da duk wata barazana — Gwamnatin Ondo
Gwamnatin ta ce ta haɗa kai da hukumomin tsaro domin ɗaukar matakan da suka dace.
Gwamnatin Jihar Ondo ta roƙi jama’a da su kwantar da hankalinsu bayan gargaɗin da Hukumar Tsaro ta DSS, ta yi na cewar wasu mayaƙan ISWAP na shirin kai hari wasu sassan jihar.
A cikin wata sanarwa, Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Mista Idowu Ajanaku, ya bayyana cewa irin waɗannan rahotanni abu ne na yau da kullum a harkokin tsaro.
- NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Sabon Haraji Da Zai Fara Aiki A 2026
- Idan Tinubu ya gaza zai yi wuya a samu shugaban da zai yi nasara — Shehu Sani
Ya ce hukumomin tsaro suna yawan musayar bayanai irin waɗannan domin daƙile duk wata barazana.
Ajanaku, ya tabbatar wa jama’a cewa gwamnati tare da hukumomin tsaro sun ɗauki matakai don kare rayuka da dukiyoyin jama’a a faɗin jihar.
“Gwamnati da hukumomin tsaro suna kan lamarin kuma suna ɗaukar duk matakan da suka dace don tabbatar da cewa Jihar Ondo ta kasance cikin aminci,” in ji sanarwar.
Ya kuma roƙi mazauna jihar da su kwantar da hankalinsu, su ci gaba da ayyukansu na yau da kullum, sannan su riƙa sanar da hukumomin tsaro idan suka ga wani abun zargi.
Kwamishinan ya ƙara da cewa gwamnatin jihar ta mayar da hankali sosai kan yankunan da ke iyakar wasu jihohi don kawar da kowace irin barazana.
“Don Allah kada ku firgita, kada kuma ku ɗauki doka a hannunku. Ku haɗa kai da gwamnati da hukumomin tsaro domin mu ci gaba da tabbatar da tsaron jiharmu,” in ji Ajanaku.