ISWAP ta harbe ’yan sanda 4 a Borno

ISWAP ta kai hari ofishin ’yan sanda na garin Gajiram da ke Karamar Hukumar Nganzai a Borno.

ISWAP ta harbe ’yan sanda 4 a Borno

Borno

Akalla ’yan sanda huɗu aka harbe da wawushe tarin makamai sakamakon mummunan harin da wasu ’yan ta’adda suka kai wani ofishin ’yan sanda a Karamar Hukumar Nganzai da ke Jihar Borno.

Ana kyautata zaton cewa mayakan Ƙungiyar ISWAP ne suka ƙaddamar da harin a ofishin ’yan sandan da ke garin Gajiram na karamar hukumar, inda suka buɗe wa ’yan sandan wuta suna bakin aiki.

A cewar majiyoyi, maharan sun kone wani sashe na ofishin ’yan sandan da suka kai hari da Yammacin ranar Juma’a.

“Gajiram a yanzu haka ba lafiya tun cikin daren jiya. Mayakan ISWAP sun kai hari ofishin ’yan sanda na Gajiram inda suka ci ƙarfin jami’an saboda tarin yawansu.

“A safiyar wannan Asabar mun gano gawarwaki huɗu kuma dukkansu ’yan sanda hudu ne. Sannan har yanzu akwai jami’an da ba gani ba,” a cewar majiyar ta ’yan bijilanti.

Wata majiyar soji ta ce lokacin da dakaru suka isa wurin da lamarin ya faru tuni ’yan ta’addan sun kama gabansu.

Sai dai har ya zuwa lokacin da wakilinmu ya aiko da wannan rahoto, rundunar ’yan sandan Borno ba ta ce uffan a kan lamarin ba.

A bayan nan dai Jihar Borno na ci gaba da fuskantar hare-haren ’yan ta’adda daga lokaci zuwa lokaci.

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan