ISWAP ta kai hari a sansanin ’yan sanda a Damboa
Daruruwan mutane sun tsere bayan harin da aka kai a garin Damboa.
Mayakan kungiyar ISWAP sun hallaka ’yan sanda uku da wasu mutane a harin da ta kai wa sansanin ’yan sandan kwantar da tarzoma da ke Damboa a Jihar Borno.
Akalla mutum hudu ne suka bakunci lahira a harin na ISWAP, baya ga wasu da dama da maharan suka jikkata a yammacin ranar Alhamis.
- Sojojin Najeriya sun kashe masu kera bom din Boko Haram
- Buhari ya ware N21.9bn domin gina asibitin duba lafiyarsa
“Kawo yanzu mutum hudu ne aka tabbatar da rasuwarsu, ciki har da ’yan sandan kwantar da tarzoma uku da wata karamar yarinya da harsashi ya same ta.
“Sun kona motoci uku na ’yan sandan kwantar da tarzoma da wata motar sintirin ’yan banga,” a cewar wata majiyar tsaro.
Wata majiyar ta bayyana wa wakilinmu cewa ’yan sandan sun rasu ne a musayar wuta tsakaninsu da mayakan da suka rika cinna wa ababen hawa wuta bayan sun kutsa cikin garin Damboa da karfin tsiya.
Majiyar ta ce kungiyar ta kuma kona ofisoshin ’yan banga da na Civilian JTF da wata motar sintiri a kan hanyar Biu, inda harsashi ya samu wata karamar yarinya, ta mutu.
Aminiya ta gano cewa harin na ISWAP a Domboa ya sa daruruwan mutane tserewa domin neman tsira, kafin daga bisani jami’an tsaron hadin gwiwa su fatattki mayakan da suka kawo hari garin.
– Sojoji sun fatattaki ISWAP a Kala-Balge –
A cikin daren ranar kuma mayakan ISWAP sun kai hari a Karamar Hukumar Kala-Balge, amma nan take sojoji suka fatattake su.
Lamarin ya faru ne da misalin karfe 11.30 na dare a garin Rann, hedikwatar Karamar Hukumar Kala-Balge.