ISWAP ta kashe ɗan sanda a Borno

Mayaƙan ISWAP sun yi garkuwa da jami’in ɗan sandan tare da iyalansa a hanyarsu ta zuwa bikin Sallah.

ISWAP ta kashe ɗan sanda a Borno

Borno

Ana fargabar cewa ƙungiyar ISWAP mai tayar da ƙayar baya a Yammacin Afirka, ta kashe wani ɗan sanda Karamar Hukumar Damboa da ke Jihar Borno.

Lamarin na zuwa ne bayan mayaƙan ƙungiyar sun yi garkuwa da jami’in ɗan sandan da kuma iyalansa a hanyar Damboa zuwa Biu a jihar ta Borno.

Majiyar Zagazola Makama, ƙwararren mai fashin baƙi kan yaƙi da tayar da ƙayar baya a yankin Tafkin Chadi, ta tabbatar da faruwar lamarin.

Majiyar ta ce ’yan ta’addan sun yi garkuwa da jami’in tsaron ne tare da matarsa da ’ya’yansa a kan hanyarsu ta tafiya bikin sallah da misalin ƙarfe 10 ma safiyar ranar Lahadi, 7 ga watam Afrilu.

Bayanai sun ce an nemi waɗanda abin ya rutsa da su an rasa amma daga bisani aka gano cewa mayaƙan ISWAP ne suka yi awon gaba da su a yankin Shokotoko da ke da tazarar kilomita Kudu da Damboa.

Sai dai daga baya da yamma an sako matar da ’ya’yansa, yayin da ’yan ta’addan suka kashe dan sandan a cewar Zagazola.

’Yan Bindiga: An miƙa wa gwamnatin Kaduna mutum 58 da aka ceto

Sarkin Zazzau ya naɗa sabbin hakimai 7

Hajjin 2025: Maniyyata za su fara ajiye N8.4m a Kaduna

Barikin Ladi: Asalin garin da yanayin rayuwar mazauna