ISWAP ta kashe fursunoninta 69 a Borno
ISWAP ta kashe mutanen ne da suka haɗa da mayaƙan Boko Haram da fararen hula da suka shafe watanni biyar a hannunta.
Ƙungiyar ISWAP mai da’awar jihadi a Yammacin Afirka, ta zartar da hukuncin kisa kan wasu fursunoninta 69 a Ƙaramar Hukumar Marte da ke Jihar Borno.
ISWAP ta kashe mutanen ne da suka haɗa da mayaƙan Boko Haram da fararen hula, wadanda suka shafe watanni biyar a hannunta.
Wata majiya mai tushe ta shaida wa ƙwararren masani kan yaƙi da tayar da ƙayar baya a yankin Tafkin Chadi, Zagazola Makama, cewa ISWAP ta zartar da hukuncin kisan ne bayan ta samu fursunonin da laifuka daban-daban.
Rahotanni sun ce kashe-kashen ya zo ne a matsayin martani ga nasarar da ISWAP ta samu a kan mayaƙan Boko Haram a baya-bayan nan.
An tattaro rahoton cewa daruruwan mutanen da ISWAP ta yi garkuwa da su, wadanda suka haɗa da mayaƙa da farar hula a halin yanzu na tsare da su a yankunan Arinna Mai Masallaci, Jibularam, da Sabon Tumbum a Ƙaramar Hukumar Marte.
Bayanai sun ce fursunonin da ke hannu ISWAP wadda ke cin karenta babu babbaka a yankin Tafkin Chadi na jiran hukunci kan laifuka daban-daban da take zargin sun aikata.
Hukuncin kisan da aka zartar ya ƙara nuna adawa mai zafi da ke tsakanin ISWAP da Boko Haram a yankunan da ke Tafkin Chadi da ma sauran wuraren da suka mamaye.