ISWAP ta sace dalibai suna zana jarrabawar NECO a Borno

Maharan sun kutsa makarantar ne da misalin ƙarfe 9 na safe, suna harbi a iska kafin su shiga ɗakin jarrabawa, inda daliban ajin karshe suke rubuta jarrabawar NECO

ISWAP ta sace dalibai suna zana jarrabawar NECO a Borno

Mayakan kungiyar ISWAP sun yi garkuwa da daliban suke tsaka da rubuta jarrabawar kammala sakandare ta NECO a garin Lassa a Karamar Hukumar Askira-Uba a Jihar Borno. 

Rundunar ’yan sandan jihar ta sanar cewa a safiyar Litinin din nan ne mayakan suka yi dirar mikiya a  Makarantar Sakandaren Gwamnati ta Je-ka-ka-dawo da ke, inda suka yi awon gaba da daukacin daliban da ke cikin aji a lokacin.

Jami’in hulɗa da jama’a na ’yan sandan, Nahum Kenneth Daso, ya shaida wa wakilinmu cewa, maharan sun shigo garin Lassa a kan babura da sunan zuwa kasuwar mako kafin su kai farmaki makarantar.

“Ranar kasuwar Lassa ce, sai suka yi amfani da hakan, suka shigo kasuwar a kan babura sannan suka nufi makarantar GDSS, Lassa, suka harbe malami ɗaya har lahira, sannan suka tafi da dukkan daliban da ke cikin aji,” in ji jami’in.

Ya ce ana zargin maharan mambobin kungiyar ISWAP ne, kuma jami’an tsaro sun tunkare su, wanda hakan ya taimaka wajen rage yawan daliban da aka sace.

Ya kara da cewa, jami’an tsaro na ci gaba da bincike a dajin da ke kewaye domin ceto waɗanda aka sace.

Shaidu daga yankin sun ce maharan sun kutsa makarantar ne da misalin ƙarfe 9 na safe, suna harbi a iska kafin su shiga ɗakin jarrabawa, inda daliban ajin karshe suke rubuta jarrabawar NECO.

Sun kara da cewa maharan sun yi awon gaba da dalibai da malamai zuwa inda ba a sani ba.

Lamarin ya faru ne bayan kwana 47 da sace daliban makarantar firamare da sakandaren Mussa guda 42 a cikin ƙaramar hukumar Askira-Uba.

Iyaye sun bayyana a ranar Lahadi cewa har yanzu masu garkuwa da yaran nasu ba su tuntube su ba, lamarin da ya ƙara tayar musu da hankali kan makomar ’ya’yansu.