ISWAP ta yi jana’izar bai-daya ga dakarunta da sojoji suka kashe a Borno

Sojojin sama na Najeriya ne suka kashe su a wasu jerin hare-hare

ISWAP ta yi jana’izar bai-daya ga dakarunta da sojoji suka kashe a Borno

Borno

Kungiyar ’yan ta’adda ta ISWAP a ranar Lahadi ta gudanar da jana’izar bai-daya ga dakarunta da sojojin sama na Najeriya suka kashe a Jihar Borno.

Rahotanni sun ce an kashe ’yan ta’addan ne a wasu jerin hare-haren da aka kai musu a kusa da garin Kwalaram da ke Karamar Hukumar Marte ta Jihar ta Borno, da safiyar Juma’a.

Wata majiyar sirri ta tabbatar da cewa ’yan ta’addan dai sun taru ne domin su kitsa yadda za su ci gaba da kai wa sojoji hari, inda jirgin sojojin sama ya yi musu ruwan wuta ta sama.

Majiyar ta ce dukkan hare-haren da aka kai wa ’yan ta’addan ta sama sun sami nasara kuma an kashe da dama daga cikinsu sannan an lalata musu gine-gine.