Italiya za ta bai wa Nijeriya jiragen yaƙi

Kafin ƙarshen shekarar 2024 ɗin nan kashin farko da adadi 6 na jiragen za su isa Najeriya.

Italiya za ta bai wa Nijeriya jiragen yaƙi

Rundunar Sojin Nijeriya na shirin karɓar wasu jiragen yaki 24 daga kamfanin kere-kere ta Leonardo da ke ƙasar Italiya.

Kakakin rundunar sojin sama, Air Vice Marshal Edward Gabkwet ne ya sanar da haka a ranar Juma’ar da ta gabata.

Gabkwet ya ce a na sa ran karban jiragen yaƙin kirar M-346 a cikin mayawa huɗu, kuma kafin ƙarshen shekarar 2024 ɗin nan kashin farko da adadi 6 na jiragen za su isa Najeriya.

Sanarwar na zuwa ne bayan ziyarar da Mataimakin Shugaban kamfanin na Leonardo, Claudio Sabatino ya kai wa babban hafsan sojin saman Najeriya a ranar laraba.

Bayanai sun ce Kamfanin Leonardo zai shafe tsawon shekaru 25 yana kula da jiragen kamar yadda bangarorin 2 suka yarje.

Wannan na daga cikin matakan da gwamnatin Najeriya ke ɗauka wajen yaƙi da matsalolin garkuwa da mutane baya ga ayyukan ta’addanci musamman na rikicin Boko Haram.