Iya Mashal Mukhtar Muhammed: Najeriya ta rasa dan kishin kasa mai gaskiya

Shugaban gidan rediyon Freedom da ke Kano kuma tsohon Kantoman mulkin soja na tsohuwar Jihar Kaduna a 1977-1978, Iya Bayis Mashal Mukhtar Muhammed (mai ritaya), ya rasu. kanensa Alhaji Aminu dalhatu wanda ya tabbatar da haka ga jaridar Aminiya ya ce, Iya Bayis Mashal Mukhtar Muhammad ya rasu ne ranar Lahadi yana da shekara 73, […]

Iya Mashal Mukhtar Muhammed: Najeriya ta rasa dan kishin kasa mai gaskiya

Shugaban gidan rediyon Freedom da ke Kano kuma tsohon Kantoman mulkin soja na tsohuwar Jihar Kaduna a 1977-1978, Iya Bayis Mashal Mukhtar Muhammed (mai ritaya), ya rasu.

kanensa Alhaji Aminu dalhatu wanda ya tabbatar da haka ga jaridar Aminiya ya ce, Iya Bayis Mashal Mukhtar Muhammad ya rasu ne ranar Lahadi yana da shekara 73, a wani asibiti da ke Landan bayan fama da rashin lafiya.

Marigayi Mukhtar Muhammad wanda shi ne Wazirin Dutse da ke Jihar Jigawa shi ne Shugaba kuma wanda ya kafa Gidan Rediyon Freedom, gidan rediyo mai zaman kansa na farko a Jihar Kano. 

An haife shi ne a ranar 11 ga Nuwamban, 1944 a garin Dutse fadar Jihar Jigawa ta yanzu. Kuma ya yi makarantar firamare a Duste, sannan ya fara sakandare a Birnin Kudu kafin ya wuce zuwa Kwalejin Barewa, inda daga can ya shiga aikin sojan sama har ya kai mukamin Iya Bayis Mashal kafin ya yi ritaya.

Baya ga kasancewarsa Kantoma Soja na tsohuwar Jihar Kaduna, Mukhtar Muhammad ya kasance wakili a Majalisar koli ta Sojin Najeriya a matsayinsa na Kwamishinan (Ministan) Ayyuka da Gidaje. 

Ya rasu ya bar mace daya da ’ya’ya bakwai.

A sakonsa na ta’aziyya, Shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda aminin marigayin ne ya bayyana Mukhtar Muhammad da daya daga cikin manyan jami’an soja na kwarai da ya taba sani.

“Mukhtar Muhammad, mutum ne mai tsayuwar daka kan gaskiya da rikon amana, kuma ya bar aikin soja ne kafin lokacin da ya kamata, saboda wannan akida tasa. ’Yan Najeriya kadan ne za su iya barin aikinsu don kare abin da suka yi imani da shi, amma Muhammad ya fita daban a wannan al’umma da ma’aikata ko jami’an gwamnati suke girmama mukami a kan mutunci,” inji Buhari a ta’aziyyarsa a ranar Litinin. 

Shugaban kasar ya fadi a sanarwar da Kakakinsa Malam Garba Shehu ya fitar cewa, marigayi Muhammad wani jigo ne abin misali ga masu son ci gaban Najeriya a kowane lokaci, inda ya tunato da “gagarumar gudunmawar’ da marigayi sojan saman ya bayar wajen cikar burin jama’arsa game da kirikiro Jihar Jigawa ta yanzu.

A ta’aziyyar Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i ya ce, marigayi Mukhtar Muhammad cikakken dan kishin kasa ne. Gwamna El-Rufa’i ya ce: “Shi tsohin gwamnan sojanmu ne da ya yi aiki da gaske wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jiharmu. A madadin gwamnati da al’ummar Jihar Kaduna, muna mika ta’aziyyarmu ga iyalansa da abokai da aminansa. Kuma Allah Ya sa Aljannar Firdausi ce makomarsa. 

kungiyar Kare Muradun Arewa (AFC), ta bayyana kaduwarta ce game da rasuwar marigayin wanda shi ne Mataimakin Shugaban Kwamitin Dattawan kungiyar.

Wata sanarwa da Kakakin kungiyar ACF, Muhammad Ibrahim ya fitar ta ce Mukhtar Muhammad wani jigo ne wajen kafuwar kungiyar tun daga farkonta. “Sojan sama ne da ake girmamawa kuma mai tsayuwa kan akidarsa, mutum ne da yake tsaye wajen tabbatar da adalci da gaskiya da daidaito a tsakanin jama’a. tsayuwar dakansa da bin ka’idoji lokacin da yake aikin sojan sama da bayan ya yi ritaya sun sanya ya yi zarra a kan tsararrakinsa,” inji ACF. 

A nasa ta’aziyyar Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Muhammadu Badaru Abubakar, ya fadi a wata sanarwa da Sakataren Watsa Labaransa Malam Bello Zaki cewa, Mukhtar Muhammed mutum ne da ake mutuntuwa a cikin soja da tsakanin jama’a, saboda gudunmawarsa wajen yi wa kasarsa hidima.

Gwamna Badaru ya shaida wa iyalai da abokan cewa marigayin ya yi kyakkyawar rayuwa tare da cimma burinsa na yi wa kasa da jama’arta hidima.

A sakonta na ta’aziyya Masarautar Dutse da ke Jihar Jigawa ta ce, marigayin Wazirin na Dutse ya bar aikin soja ne saboda nuna rashin amincewa da juyin mulkin da Janar Ibrahim Babangida ya yi wa Janar Muhammadu Buhari a 1985.

Galadiman Duste Alhaji Basiru Muhammadu Sunusi ne ya shaida wa Aminiya haka a ranar Talata inda ya ce: “Marigayi Wazirin cikakken mai goyon bayan Buhari ne. Marigayi Mashar Mukhtar ya bar aikin soja ne saboda nuna rashin jin dadi lokacin da Babangida ya kawar da gwamnatin Buhari.

Ya ce masarautar ta yi babban rashi na marigayin, “Marigayi Waziri yana daya daga cikin iyayen da suka aza harsashin zamanantar da garin Dutse,” inji shi.

Shugaban Majalisar Gwamnonin Arewa, Gwamnan Jihar Borno, Alhaji Kashim Shettima, ya ce rasuwar Mashal Mukhtar,”Aba ce mai girgizarwa ganin ta zo ne bayan ’yan watanni da rasuwar Alhaji Yusuf Maitama Sule. Rasuwar Mashal Mukhtar babban rashi ne ga Arewa. Dattijo ne tsayayye da yake son Arewa ta rika gasa a kowane fage na harkokin kasar nan. Saboda cikakkiyar kaunar da yake yi ga Arewa ce ya zuba jari wajen kafa gidan rediyon Freedom, duk da cewa a lokacin harkar gidan rediyo ba mai kawo riba ba ce.”

Tsohon Janar Manajan Rediyon Freedom, Malam Umar S. Tudun-Wada, ya ce “Duk da kasancewarsa tsohon soja, marigayi Mashal Mukhtar Muhammad mutum ne mai saukin kai.”

Shugaban Majalisar Malamai ta Jihar Kano, Sheikh Ibrahim Khalil, ya bayyana Mashal Mukhtar da dan kishin kasa da ya yi aiki sosai don ci gaban kasar nan.

Wani Farfesa a sashin Nazarin Aikin Jarida a Jami’ar Bayero, Kano, Balarabe Maikaba, ya yi kira ga Gwamnatin Jihar Jigawa da Tarayya su sanya wa wani muhimmmin wuri sunan Mukhtar Muhammad domin a rika tunawa da shi.

kungiyar Tsoffin Sojoji ta Najeriya (RANOA), ta nuna alhini ne da kaduwa kan rasuwar Mashal Mukhtar, inda Kakakinta Kyaftin Yusuf Abdulmalik ya bayyana marigayin a wata takardar sanarwa da jajirtaccen soja dan kishin kasa kuma jagora a duk wani aiki na ci gaban al’umma. Ta ce rasuwar Mukhtar babban rashi ne ga kasa baki daya, idan aka lura da dimbin gudunmawar da ya bayar ga cin gaban jama’a a lokacin da yake aikin soja da bayan ya yi murabus. 

A ta’aziyyarsa kan rasuwar marigayi, Sardaunan Dutse, Alhaji Bello Maitama Yusuf ya bayyana shi da dan kishin kasa wanda yayi kokari sosai wajen ganin Nijeriya ta samu ci gaba da kuma wanzuwar zaman lafiya da kaunar juna.

Sanata Bello Maitama ya bayyana haka ne a zantawarsu da wakilin mu bayan kammala jana’izar marigayin, inda ya ce kasar nan ta yi babbar asarar jarumi kuma mai son taimakon jama’a ba tare da nuna gajiyawa ba. Ya ce Iya Mashal Mukhtar Muhammad mutum ne mai gaskiya wajen gudanar da duk wata hidima ta jama’a, wanda ba ya son a tauye hakkin wani a duk inda ya samu kansa.

A nasa ta’aziyyar, wani dan kasuwa Alhaji Ubale Kirilla ya ce Wazirin Dutse, mutum ne mai saukin kai da taimakon jama’a, kuma ya yi ayyuka masu yawa da ba za a taba mantawa da shi ba, inda ya yi masa addu’ar samun rahamar Allah.

Shugabar Kamfanin Bintus Nigeria Limited, kuma fitaciyar ’yar Jam’iyyar APC a Jihar Jigawa Hajiya Binta Shu’aibu Gwaram, ta ce Najeriya za ta dade ba ta manta da gudunmawar da Mashal Mukhtar Muhammad ya bayar wajen samun zaman lafiya da ci gaban kasa da kaunar juna ba.

A shekaranjiya Laraba da yamma ce aka dawo da gawar marigayin wadda ta samu rakiyar matarsa Hajiya Rabi Mukhtar Muhammad da ’ya’yansa Abba da Mukhtar, inda aka yi jana’izarsa a kofar Fadar Sarkin Kano.

Gwamnonin Kano da Jigawa Abdullahi Umar Ganduje da Muhammad Badaru Abubakar da Shugaban Ma’aikata na Fadar Shugaban kasa Alhaji Abba Kyari wanda ya jagorancin wakilan Gwamnatin Tarayya ne suka tarbi gawar a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano da misalin karfe 7:35 na yamma. 

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aike da sakon ta’aziyya wanda Abba Kyari ya mika ga Mai martaba Sarkin Dutse Alhaji Nuhu Muhammad Sunusi, sai dai bai bayyana abin da sakon ya kunsa ba.

Da yake mayar da jawabi Sarkin Dutse ya ce marigayi Wazirin na Dutse babban aminin Shugaban kasar ne, kuma yana daga cikin wadanda suka jagoranci yi wa Shugaba Buhari addu’o’i a masarautar lokacin yake jinya a waje.

Gwamnoni da shugabannin al’umma na ci gaba da aikewa da sakon ta’aziyya kan rasuwar marigayin, inda kowa ke bayyana shi da dan kishin kasa mai gaskiya da rikon amana.