Iyalan Abacha sun gargaɗi Babangida kan ɓata sunan mahaifinsu

Iyalan marigayin sun buƙaci ‘yan Najeriya su watsi da maganganun da ake yaɗa a kan mahaifinsu.

Iyalan Abacha sun gargaɗi Babangida kan ɓata sunan mahaifinsu

Iyalan marigayi Janar Sani Abacha, sun gargaɗi Tsohon Shugaban Mulkin Soja, Janar Ibrahim Babangida, da ya daina faɗin maganganun da ka iya ɓata sunan mahaifinsu.

A cikin wata sanarwa da Mohammed Abacha, ya fitar a madadin iyalan marigayin a ranar Lahadi, sun musanta iƙirarin da Babangida ya yi a cikin littafinsa mai suna ‘A Journey in Service’.

Ya ce Janar Abacha ne, ya ke da alhakin soke zaɓen shugaban ƙasa na ranar 12 ga wata Yunin 1993.

“Duk wani yunƙuri na ɗora wa Janar Sani Abacha laifin soke zaɓen, wanda a lokacin ya kasance babban jami’in soja a mulkin Babangida, ƙoƙari ne na sauya tarihi da gangan.

“Shekaru da dama, wasu mutane na ƙoƙarin ɓata haƙiƙanin abin da ya faru a wannan lokaci a tarihin dimokuraɗiyyar Najeriya,” in ji sanarwar.

Iyalan Abacha sun jaddada cewa a lokacin da aka soke zaɓen, Janar Abacha ba shi ne Shugaban Ƙasa ko Babban Kwamandan Askarawan Najeriya ba.

Sun ce Babangida ne, ya ke da cikakken iko, kuma shi kaɗai ne ke da alhakin duk wani hukunci da gwamnatinsa ta yanke.

“Hukuncin soke zaɓen ya fito ne daga gwamnatin Janar Ibrahim Babangida, wanda yake a matsayin Shugaban Ƙasa, yana da cikakken iko kuma shi ne ke da alhakin duk wani abu da gwamnatinsa ta aikata,” in ji sanarwar.

Haka kuma, iyalin Abacha sun yi kira ga ‘yan Najeriya da su guji “ƙagaggun labarai da ake ƙirƙira don karkatar da tunanin jama’a saboda wasu muradu na siyasa ko na ƙashin kai.”

Sun jaddada cewa, “Ba za mu yarda a ɓata tarihin mahaifinmu da wasu zarge-zargen banza da aka ƙirƙira don kare waɗanda suka aikata laifin ba.”

“Mun kuma ga dacewar tunatar da mutane cewa a lokacin da rayuwar Janar Babangida ta shiga hatsari, Janar Abacha ne, ya kawo masa ɗauki, ya tabbatar da cewa ba a cutar da shi ba,” in ji iyalan.

A ƙarshe, sun soki littafin ‘A Journey in Service’, inda suka ce littafin bai bayar da sahihin tarihin abubuwan da suka faru ba.

“A cewar wani da ya yi sharhi a kan littafin, gaskiya, amana ba halaye ba ne da za a alaƙanta su da marubucin ba,” in ji su.