Iyalan Bello Boɗejo sun buƙaci sojoji su saki shi

Iyalan Shugaban Kungiyar Makiyaya ta Miyetti Allah Kyautal Hore, Alhaji Bello Boɗejo sun bukaci Shugaba Tinubu Tinubu ya sa baki sojoji su sako shi

Iyalan Bello Boɗejo sun buƙaci sojoji su saki shi

Iyalan Shugaban Kungiyar Makiyaya ta Miyetti Allah Kyautal Hore, Alhaji Bello Boɗejo sun bukaci Shugaba Tinubu Tinubu ya sa baki sojoji su sako shi.

Matarsa, Hajiya Hauwa Bello Boɗejo ta roƙi hukumomi da kungiyoyin ƙasashen duniya da kungiyoyin fararen hula da masu faɗa a ji a Nijeriya da su sa baki cikin lamarin mijin nata.

Aminiya ta ruwaito cewa sojoji daga Runduna ta 177 da ke Keffi a Jihar Nasarawa ne suka yi dirar miliyan a gidan Bello Boɗejo suka yi awon gaba da shi, daga bisani suka damƙa shi ga Hukumar Leƙen Asiri ta Soji (DIA).

Hajiya Hauwa ta shaida wa taron manema labarai a Abuja cewa tsarewar da aka yi masa ba tare da wani ƙwaƙƙwaran dalili ba, ya jefa shi da su duka cikin tashin ha hankali.

Ta ce rashin lafiyar da yake fama da ita ta ƙara tsananta, don haka ta roki Tinubu ya sanya baki a lamarin domin sojoji su sako mijin nata.

Ta bayyana cewa mijin nata masoyin zaman lafiya ne kuma mutum ne mai bin doka ne, sannan yana sa kishin ƙasa, don haka ya cancanci mutuntawa.

Hajiya Hauwa wadda ke zubar da hawaye ta ce haka a kwanakin baya sojoji suka tsare mijin nata tsawon watanni biyar ba tare da wata ƙwaƙƙwarar tuhuma ba ko dalili.

Ta ce bayan an sako shi ne ya fara fama da rashin lafiya inda a ƙarshe a aka kai shi kasar waje jinya, inda likitoci suka tabbata da cewa halin da ta ya tsinci kansa a lokacin da yake tsare ne ya jefa shi cikin wannan yanayi.

Hajiya Hauwa ta ce ana murnar cewa ya fara murmurew tare da ƙoƙarin manta abin da ya faru a baya kuma sai sojoji suka sake kama shi a cikin dare a gaban ’ya’yansa, daga baya ne kuma sunlka mika shi ga DIA.

Don haka ta roki Shugaba Tinubu ya shiga lamarin domin ganin sojojin sun sako mijin nata l, Alhaji Bello Boɗejo ya dawo cikin iyalansa.