Iyalan da suka haifi ’ya’ya maza 12 na hankoron samun ’ya mace

Wasu ma’aurata da ke zaune a Yammacin Jihar Michigan da ke da ’ya’ya maza 12, suna sa ran haohuwar dan sun a 13, amma sun ce za su yi mamakin kasancewarsa namiji, kamar yadda yadda kafar yada labarai ta The Grand Rapids Press ta ruwaito. Ma’auratan Jay da Kateri Schwandt na sa ran haihuwar dan […]

Iyalan da suka haifi ’ya’ya maza 12 na hankoron samun ’ya mace
Iyalan da suka haifi ’ya’ya maza 12 na hankoron samun ’ya mace

Wasu ma’aurata da ke zaune a Yammacin Jihar Michigan da ke da ’ya’ya maza 12, suna sa ran haohuwar dan sun a 13, amma sun ce za su yi mamakin kasancewarsa namiji, kamar yadda yadda kafar yada labarai ta The Grand Rapids Press ta ruwaito.

Ma’auratan Jay da Kateri Schwandt na sa ran haihuwar dan sun a 13 nan da 9 ga watan Mayun badi
Uwargida Kateri ta ce:”Idan har muka haifi ’ya mace, ina ganin za mu cika da mamaki.”
Shi kuwa maigida Jay Schwandt cewa, ya yi, zai yi matukar farin cikin samun ’ya mace, amma dai abin da kawai muka fi bukata shi ne: “samun lafiyayyen jariri.”\
Wadannan iyalai suna zaune ne a garin Rockford da ke cikin Jihar Michigan, sannan dan sun a 12, tucker, an haife shi ne a ranar 4 ga Agustar 2013, shi kuwa baban dan su an haife shi ne shekra 22 da suka wuce.