Iyalan Inyas sun ziyarci Sheikh dahiru Bauchi don jajanta masa kan rashin tsaro a Arewa

Iyalan Sheikh Ibrahim Inyas daga kasar Senegal sun ziyarci Sheikh dahiru Bauchi domin jajantawa tare da yin addu’a game da matsalolin da suke faruwa a jihohin Borno da Yobe da sauran yankunan arewacin kasar nan.Iyalan sun kai ziyarar ce bayan da shugabannin darikar Tijjaniyya na Afirka suka gudanar da taron mutum miliyan biyu da rabi […]

Iyalan Inyas sun ziyarci Sheikh dahiru Bauchi don jajanta masa kan rashin tsaro a Arewa
Iyalan Inyas sun ziyarci Sheikh dahiru Bauchi don jajanta masa kan rashin tsaro a Arewa

Iyalan Sheikh Ibrahim Inyas daga kasar Senegal sun ziyarci Sheikh dahiru Bauchi domin jajantawa tare da yin addu’a game da matsalolin da suke faruwa a jihohin Borno da Yobe da sauran yankunan arewacin kasar nan.
Iyalan sun kai ziyarar ce bayan da shugabannin darikar Tijjaniyya na Afirka suka gudanar da taron mutum miliyan biyu da rabi a garin Dutse ta Jihar Jigawa don gudanar da addu’o’in neman zaman lafiya ga Najeriya.
Tawagar a karkashin Sheikh Mukhtari Ibrahim Inyas da ta kunshi iyalai da surukan Sheikh Inyas, ta zo yi addu’o’in fatar alheri, tare da ci gaban darikar Tijjaniyya a duniya baki daya.
A jawabinsa ga manema labarai Sheikh dahiru Bauchi ya ce a wannan lokaci an samu ci gaba sosai wajen haddace Alkur’ani Mai girma, saboda a baya sai an yi tattaki zuwa wasu kasashe ko jihohi don haddace Alkur’ani amma yanzu a gidansa kurum suna yaye mahaddata masu yawa, kuma a Sakkwato za su yaye mahaddata 80 nan ba da jimawa ba, haka lamarin yake a Bidda da Kano da Kaduna da Katsina da sauran jihohin Najeriya da kasashen makwabta.
Ya ce darikar Tijjaniyya ta shiga wurare da dama a duniya, wanda ke son ya taimaki Allah ya taimaki addininsa, duk wanda ba zai yi ba kuma ya zuba ido idan ya ce zai tsangwami Musulunci da Musulmi zai karye.
Sheikh dahiru Bauchi ya ce taron da suka gudanar a Jigawa na sama da mutum miliyan biyu da rabi ba tare da hannun hukuma ba, sun yi sun gama lafiya kowa ya koma gida lafiya. Ya ce a baya sun gudanar da irin wannan taro a Minna da Sakkwato da Adamawa, kuma suna samar da abinci da wurin kwana da tsaro ingantacce ba tare da neman wani abu wajen wani attajiri ko basarake ko dan siyasa ba, sai don neman yardar Allah kurum.
Ya shawarci ’yan Najeriya su gyara ayyukansu su daina zagin shari’ar Musulunci da kafirta Musulmi da zagin waliyai don abubuwa ne da Allah ba Ya so kuma duk wanda ya ce zai yaki masoya Allah da ManzonSa lallai zai shiga cikin mummunan matsayi na kaskanci a duniya da Lahira.