Iyalan mamatan da hadarin mota ya haddasa a Legas sun koka da gwamnati

Iyalan mamata uku da suka riga mu gidan gaskiya a sakamakon hadarin da babbar mota mai dauke da kwantena ta yi a Legas kwanakin baya, sun koka da gwamnatin Jihar Legas, saboda ta wahalar da su kafin a ba su gawarwakin ’yan uwansu su binne.Hadarin dai ya faru ne a yayin da wata babbar mota […]

Iyalan mamatan da hadarin mota ya haddasa a Legas sun koka da gwamnati
Iyalan mamatan da hadarin mota ya haddasa a Legas sun koka da gwamnati

Iyalan mamata uku da suka riga mu gidan gaskiya a sakamakon hadarin da babbar mota mai dauke da kwantena ta yi a Legas kwanakin baya, sun koka da gwamnatin Jihar Legas, saboda ta wahalar da su kafin a ba su gawarwakin ’yan uwansu su binne.
Hadarin dai ya faru ne a yayin da wata babbar mota dauke da kwantena ta subuto daga kan gadar sama, ta danne wata karamar mota baka kirar Toyota Corolla, dauke da mutum uku, wadanda nan take suka mutu.
Mamatan, wadanda mazauna Agege ne, sun hada da direban motar mai suna Kamilu, sai Abubakar Sulaiman, wanda aka fi sani da Baba, sai kuma Alhaji Umar Fakaci; sun hadu da ajalinsu ne a sa’ilin da suke komowa daga unguwar Apapa.
Yayan direban motar mai suna Ahmad, ya shaida wa Aminiya cewa a talabijin ya soma ganin labarin hadarin, kafin daga bisani a kira shi ta waya a shaida masa cewa kaninsa Kamilu ya yi hadari tare da abokakan tafiyarsa. Ya yi korafi bisa tsaikon da suka fuskanta kafin a ba su gawar mamatan, inda ya ce duk lokacin da aka ce su je su karbi gawa daga dakin ajjiyar gawarwarkin sai an samu tsaiko. “Kamata ya yi wadanda abin ya shafa su rika la’akri da tanade-tanaden addinin Musulunci wajen suturta gawa. Gwamnan Legas Akinwumi Ambode ya ziyarci inda hadarin ya afku sannan ya gana da iyalan mamatan kwana daya da faruwar hadarin a offishinsa kafin a yi jana’izarsu. Ya kuma ba da umarnin tuhumar direban babba motar, Wasiu Adeleke da laifin tukin ganganci da kuma kashe rayuka.” A cewar Ahmad Faki.
Shi kuwa Abokin mamaci Umar Ibrahim Faki, kira ya yi da a dauki matakan da ya kamata a kan manyan motocin da ke zirga-zirga a cikin jama’a, domin kare rayuka da dukiyoyinsu.
Babban jami’in ’yan sandan shiyyar Surulere, CSP Monday Abonike ya tabbatar da kame direban motar da ta dauko kwantenar, Wasiu Adeleke.