Iyalan Mandela da ’yan siyasa na takaddamar amfani da sunansa a tallata manufa da haja

Iyalan marigayi Gwarzon Afirka ta Kudu, Nelson Mandela da ’yan siyasa da masu tallar haja, na takaddama kan amfani da sunansa wajen yada manufa da tallata haja. Wannan kuw aya biyo bayan rasuwar gwarzon al’ummar ne.Bayan mutuwar Nelson Mandela, yana dan shekara 95, iyalansa da Jam’iyyarsa ta ANC da Cibiyar kare manufofinsa sun yunkuro wajen […]

Iyalan Mandela da ’yan siyasa na takaddamar amfani da sunansa a tallata manufa da haja

Iyalan marigayi Gwarzon Afirka ta Kudu, Nelson Mandela da ’yan siyasa da masu tallar haja, na takaddama kan amfani da sunansa wajen yada manufa da tallata haja. Wannan kuw aya biyo bayan rasuwar gwarzon al’ummar ne.
Bayan mutuwar Nelson Mandela, yana dan shekara 95, iyalansa da Jam’iyyarsa ta ANC da Cibiyar kare manufofinsa sun yunkuro wajen gasar wanda zai ci gadonsa.
Gadonsa dai an bayyana za a raba shi ne ga ’ya’yansa da jikoki da tattaba kunne, wadanda a kalla yawansu ya kai 30, inda mafi yawansu ke amfani da sunan wajen tallata haja a kasuwanni, har ma tufafi da shirye-shiryen talabiji da kwalaben giya.
Tun a bara aka fara tafka shari’a tsakanin lauyan Mandela, kuma tsohon abokinsa George Bizos da ’ya’yansa mata da sauran abokan huldarsa, inda iyalan ke bukatar kawar da sauran mutanen da cin gajiyar kamfanonin da ke amfani da tambarinsa a zayyana da kayayyakin kawa.
A bayanan da ke kunshe a takardar kara da Bizos ya gabatar a kotu, ya zargi ’ya’yan Mandela biyu, wato Makaziwe Mandela da Zenani Dlamini da kokarin mamaye Cibiyar Kula da Manufiofin Mandela, tun a shekarar 2005, ta yadda za su zama amintattun cibiyar ba tare da snain Mandela ba.
A cewar Bizos da gungun wadanda ake son kawarwa daga cibiyar, “ran Mandela ya baci a lokacin da ya samu labarin abin da ‘’ya’yansa suka aikata.”

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan