Iyalan Mursi sun ce ba zai mika wuya ga gwamnati ba

Iyalan hambararren Shugaban Masar Mohammed Mursi sun fadi a ranar Lahadin da ta gabata cewa ba zai kulla wata yarjejeniya ko ya mika wuya saboda gallazawar da sojoji suke yi wa ’ya’yan kungiyarsa ta Ikhwanul Muslimina ba. Kamfanin Dillancin Labarai na Ingila (Reuters) ne ya ruwaito haka a sakon iyalan na Barka da Babbar Sallah.Mohammed […]

Iyalan Mursi sun ce ba zai mika wuya ga gwamnati ba

Mohammed MursiIyalan hambararren Shugaban Masar Mohammed Mursi sun fadi a ranar Lahadin da ta gabata cewa ba zai kulla wata yarjejeniya ko ya mika wuya saboda gallazawar da sojoji suke yi wa ’ya’yan kungiyarsa ta Ikhwanul Muslimina ba. Kamfanin Dillancin Labarai na Ingila (Reuters) ne ya ruwaito haka a sakon iyalan na Barka da Babbar Sallah.
Mohammed Mursi wanda shi ne zababben shugaban kasa na farko a karkashin mulkin dimokuradiyya a Masar sojoji sun kifar da gwamnatinsa ne a watan Yulin da ya gabata bisa hujjar jama’a suna zanga-zangar nuna rashin amincewa da gwamnatinsa. Kuma tun daga lokacin mahukuntan kasar suka kaddamar da farautar ’ya’yan kungiyar Ikhwanul Muslimina, inda suka kashe daruruwa da suke zanga-zangar zaman dirshan a wasu tantuna da kuma lokacin zagaye tare da kama masu kishin addini da ’ya’yan kungiyar sama da dubu biyu.
Tun da aka yi wa Mursi juyin mulki ake tsare da shi a wani wuri da ba  a sani ba, kuma har zuwa yanzu ba a ganinsa. Kuma ana kokarin gabatar da shi  a gaban kotu ranar 4 ga Nuwamba mai zuwa bisa tuhumar tunzura jama’a.
Sakon iyalan Mursi da aka aika ta kafar sadarwar kungiyar mai suna www.ikhwanonline.com ya ce, “Shugaban ba zai ja da baya ba, ko ya kulla yarjejeniya ko ya mika wuya musamman bayan mutane da dama sun yi shahada, an raunata wasu, an kashe wasu, kuma wasu sun bace.”
Sun kara da cewa, “Duk yadda suka kai ga boye, Shugaban kasar ba zai ja da baya ba a kokarinsa na kare hallacin gwamnatinsa, koda zai kai ga rasa ransa.”
Mursi da shugabannin Ikhwanu sun zargin sojojin kasar da shirya juyin mulki don dakile nasarar juyin juya-halin shekarar 2011 da ya yi waje da Shugaba Hosni Mubarak.
Sojojin sun ce sun gabatar da wani shiri da suka ce zai kai ga gudanar da zabe na gaskiya a kasar, amma Ikhwanu ta ce ba za ta shiga zaben ba, domin yin haka zai ba juyin mulkin halacci.
A makon jiya magoya bayan Mursi sun fafata da abokan adawarsu inda kafafen watsa labaran kasar suka ce mutum 57 sun mutu.