Iyalan mutum 8 da aka kama a garin Gauraka sun koka bayan mako biyu ba labarinsu

Iyalai da wasu dangi na mutum 8 da aka kama a garin Gauraka da ke karamar Hukumar Tafa ta Jihar Neja kamar mako biyu da ya gabata, sun koka a kan ci gaba da tsare jama’ar, bayan yunkurin gano inda suke ko kuma jin labarinsu ba tare da nasara ba. Wakilinmu wanda ya ziyarci garin […]

Iyalan mutum 8 da aka kama a garin Gauraka sun koka bayan mako biyu ba labarinsu


Iyalai da wasu dangi na mutum 8 da aka kama a garin Gauraka da ke karamar Hukumar Tafa ta Jihar Neja kamar mako biyu da ya gabata, sun koka a kan ci gaba da tsare jama’ar, bayan yunkurin gano inda suke ko kuma jin labarinsu ba tare da nasara ba.

Wakilinmu wanda ya ziyarci garin a ranar Talata da ta gabata, ya samu labarin cewa kama mutanen ya biyo bayan wani samame ne da wasu jami’an tsaro da ake kyautata zaton na farin kaya ne, suka gudanar a garin a ranar Alhamis, 11 ga wannan wata da misalin karfe 3 da rabi na rana.

Wasu da suka zanta da Aminiya sun bayyana cewa jami’an tsaron wadanda suka isa garin cikin motoci 5 sanye da safar fuska, sun kama uku daga cikin mutanen ne a cikin shagonsu na dinki da ke tsakiyar garin, a yayin da ragowar kuma da ya hada da mai sana’ar silin na POP da dan hidimar kasa (NYSC) da direban tanka da wani dan kasuwa, sai kuma wani mai yankan farce da ke yi wa daya daga cikinsu aiki a jikin shagon wanda ke matsayin majalisa, a cewar majiyar.

“Da farko sun bukaci wadanda suka kaman da su kwanta a kasa sannan suka rufe masu fuska kafin fara aiwatar da bincike a cikin shagon, sai kuma suka wuce da su zuwa gidan dan kasuwar, wanda bisa ga dukkan alamu shi ne suke nema,” a cewar majiyar.

Azantawarsu da Aminiya, matan dan kasuwar sun yi ikirarin cewa, mijinsu na gudanar da sana’ar sayar da atamfa da takalma a garin gabanin ya koma Jihar Taraba da harkar a shekarun baya, inda kuma yake ziyartarsu bayan kamar wata daya.

“Mijinmu ya zo a ranar 28 ga watan Disamba don zama da mu na ’yan kwanaki a lokacin da wannan ibtila’in ya faru, kuma daga nan ba mu sake jin duriyarsa ba ko sanin inda ya ke tun lokacin,” inji matar.

Bayanai sun ce daya daga cikin motocin da aka je aikin da su, ta jima tana zirga-zirga a cikin garin gabanin ragowar su shigo, inda ake zargin cewa yunkuri ne na sunsunar wayar mutumin da wani da ke cikin motar ya aiwatar. Wasu da aka zanta da su, sun tabbatar da cewa, tini iyalan wadanda aka kaman suka dau lauya inda ya rubuta wasika zuwa ga hukumar jami’an tsaron farin kaya na SSS, reshen jihar da kuma aikawa da kwafin takardar zuwa hedikwatarsu ta Abuja, inda suke neman da a sake mutanen da aka kaman ko kuma a kai su kotu.

Hakan a cewar bayanin, kari ne a kan wasu wasiku da aka rubuta zuwa ga Gwamnatin Jihar Neja da masarautar Suleja da kuma babban ofishin ’yan sanda na karamar hukumar don sanar da su faruwar lamarin. Da aka tuntube shi, babban jami’in ’yan sanda na shiyyar Suleja, A.C.P Ilyasu kwarbai wanda ya ce ya samu labarin faruwar lamarin, ya kara da cewa babu hannun ’yan sanda a cikin aikin.