Iyalan mutum guda mai cin buhun shinkafa kullum

Wani Ba’Indiye mai shekara 72 da yake zaune a Jihar Mizoram da ke Arewa maso Gabashin kasar, yana da iyalai 181, wadanda aka ce su ne iyali mafi yawa da ke zaune a tare wuri guda. Kuma iyalan sun hada da matansa 39 da ’ya’ya 94 da surukai matan ’ya’yansa maza 14 da jikoki fiye […]

Iyalan mutum guda mai cin buhun shinkafa kullum

Wani Ba’Indiye mai shekara 72 da yake zaune a Jihar Mizoram da ke Arewa maso Gabashin kasar, yana da iyalai 181, wadanda aka ce su ne iyali mafi yawa da ke zaune a tare wuri guda. Kuma iyalan sun hada da matansa 39 da ’ya’ya 94 da surukai matan ’ya’yansa maza 14 da jikoki fiye da 40.

Wadannan iyalai da aka kimanta yawansu da 181 suna dada karuwa yayin da ’ya’yansa maza da mata ke haihuwa wasu ’ya’yan.

Dattijon mai suna Ziona yana tare da iyalansa 181, inda suke zaune a wani katafaren gidansa da aka gina mai launin rawaya, mai hawa hudu tare da dakuna fiye da 100.

Wadannan iyalai, matakai hudu suka hadu (’ya’ya da jikoki). Kuma sun himmatu wajen aikin gona don magance matsalar abincin da suke bukata. Abin da ya rage wa Ziona shi ne ya akfa makarantar kashin kansa, domin ‘’ya’yansa, a ceewar rrahoton wata kafar sadarwar shafin intanet, kamar yadda Khaleej Times ta ruwaito.

daukar dawainiyar ciyar da wadannan iyalai ba abu ne mai sauki ba, domin suna cin buhun shinkafa mai nauyin kilo 50 a kowace rana. Ayyukan gida ana raba wa ne tsakanin matan, inda babbarsu, tsohuwar matarsa ke tsara yadda za a yi ayyuka tare da sanya ido wajen gudanar da su.

Ziona na cikee da farin ciki daukar dawainiya wadannan dimbin iyalai nasa, inda yake ganin ya yi babbar sa’a. Ya ce yana auren mata ne daga talakawan kauye don ya dauki nauyinsu.