Iyalan Oruwari suna cikin alhinin rashin OB Lulu-Briggs

  Wata 5 ba a san inda yake ba – Iyalan Oruwari   Iyalan wani attajiri a Jihar Ribas, hamshakin basaraken dan kasuwa mai taimakon talakawa, Cif OB Lulu-Briggs na cikin damuwa, saboda rasuwarsa. Basaraken shi ne mai sarautar Oruwari Briggs  da ke yankin War-Canoe House da ke Abonnema a Karamar Hukumar Akuku-toru Jihar Ribas. Attajirin […]

Iyalan Oruwari suna cikin alhinin rashin OB Lulu-Briggs
  •   Wata 5 ba a san inda yake ba – Iyalan Oruwari

 

Iyalan wani attajiri a Jihar Ribas, hamshakin basaraken dan kasuwa mai taimakon talakawa, Cif OB Lulu-Briggs na cikin damuwa, saboda rasuwarsa.

Basaraken shi ne mai sarautar Oruwari Briggs  da ke yankin War-Canoe House da ke Abonnema a Karamar Hukumar Akuku-toru Jihar Ribas.

Attajirin mai sana’ar mai ya rasu ne a hanyarsa ta zuwa kasar Ghana a ranar 27 ga Disamba 2018. Kimanin wata biyar kenan da rasuwar, in ji daya daga cikin wadanda suke taimakawa sarkin Oruwari Briggs War-Canoe House a garin Abonnema, iyalan sun ce har yanzu su na jiran su ji bayani game da rasuwar mahaifinsu.

A yankin Kalabari inda masarautar take wanda aka sarin kabilun yankin ke suna gabar ruwa ne a jihar, babban Sarkin yankin ya bukaci a sanarwa matar marigayin halin da mijinta yake ciki da sauran iyalansa game da rasuwar basaraken, amma masarautar Oruwari Briggs War-Canoe house, sun ce an boye masu halin da ake ciki game da rasuwar shugaban su.

Iyalan sun wallafa damuwar su a jaridar national daily, inda wadanda suka rattaba hannu suka hada da: Cif AB Ajumogobia, Cif Ibim Briggs, Cif Jacob Dokubo Briggs, Cif Solomon Briggs, Cif Festus Captain Briggs , Cif Dumo Membere da Cif C.F.L. Mambobin masarautar sun ce, suna cikin rashi game da rashin sanin inda shugaban su yake tun lokacin da matarsa Seinye Lulu-Briggs, ta sanar da rasuwarsa a ranar 27 ga Disamba 2018 yayin tafiyarsa zuwa Ghana.

Iyalan sun ce, har yanzu sun kasa fahimtar cewa, dan’uwan su yana raye ne ko ya mutu, tun da ya yi tafiya da matarsa wata biyar da suka wuce ba su kara jin doriyarsa ba ko gawarsa, a takardar dakin ajiye gawa ba a bayyana takardar rashin lafiyar da ya yi wanda ya yi sanadiyyar mutuwarsa ba.

Rukunin mutanen sun ce, sun samu bayanan da ba a tabbatar ba game da rasuwar marigayin, sai dai kawai matarsa ce take ta yada rahotan rasuwar mijinta, wanda suka ce suna tare da marigayin a ranar rasuwar Cif din amma ba a samu wani dalilin rasuwarsa ba.

Iyalan sun ce, ba bu wata takardar shaidar asibiti game da mutuwar marigayin da kuma inda aka adana gawar, komai an yi shi ne a sirrance saboda an sa su a cikin duhu kuma aka yi watsi da halin da ake ciki na rashin sanin inda marigayin yake.

Iyalan sun bayyana damuwar su ne game da rashin sanin halin da ake ciki na rashin basaraken da ke shugabantar masarautar Oruwari Briggs House, an dai shirya bikin birne basaraken wanda aka shirya a Ghana da kuma wata liyafa ta musamman da aka shirya a jami’ar jihar duk ba tare da sanin iyalansa ba.

An dai samu sanarwar rasuwar basaraken ne kawai daga wajen matarsa, inda kawai ita kadai ta dauki ragamar shirin bikin birne basaraken, wanda hakan ya zama wani sabon abu ga dansa a al’adar Kalabari, ganin ba haka tsarin masarautar yake ba, ace mata ce zata sanar da rasuwar mijinta ga sauran iyalan. Yayin da a al’adance iyalan wanda ya rasu ne ke shirya duk wasu bukukuwan birnen mamaci.

Rasuwar Cif OB Lulu-Briggs, ta razana jama’a da dama kasancewarsa  mutum mai taimakon jama’a. Ya kasance mutum mai taimakon jama’a a fannin kiwon lafiya da ilimi musamman ’yan jihar Ribas.