Iyaye a kula da tarbiyyar yara – Hajiya Safiya
TarihinaDa farko dai sunana Safiya Tahir Abdullahi, ni ’yar asalin Jihar Bauchi ce. Kuma a can aka haife ni a wata unguwa da ake kira Unguwar Alkali Aminu. Sunan mahaifina Jafaru Tahir, mahaifiyata kuma Maryam Tahir.Ina da shekara takwas na fara karatun firamere a Babban Mutum daga shekarar 1972 zuwa 1978. Daga nan na shiga […]
Tarihina
Da farko dai sunana Safiya Tahir Abdullahi, ni ’yar asalin Jihar Bauchi ce. Kuma a can aka haife ni a wata unguwa da ake kira Unguwar Alkali Aminu. Sunan mahaifina Jafaru Tahir, mahaifiyata kuma Maryam Tahir.
Ina da shekara takwas na fara karatun firamere a Babban Mutum daga shekarar 1972 zuwa 1978. Daga nan na shiga makaratar ’yan mata ta Bauchi (GSS), ina aji hudu ne aka cireni don a mayar da makaratar kimiyya. Mu a lokacin ba bangaren muke yi ba, duk da gwamnati ta yi umarnin kowa ya koma makaratar da ke kusa da gidansu. Saboda haka aka mayar da ni makaratar ’yan mata ta Azare. Bayan na kamala, na wuce mala karatun share fagen jiga jami’a wato (IJMB) shekara biyu a kwalejin fasaha da kimiyya. Daga nan na samu gurbin karatu a Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya. Na yi shekara uku na kammala digirina na farko, ina shekarar karshe ne aka yi mini aure wanda hakan ya sanya lokacin bautar kasa da aka turani tsohuwar Jihar Bendel na dawo Sakkwato, wurin da mijina yake malanta a Jami’ar Usman danfodiyo. Lokacin da nake bautar kasa ne na samu haihuwar fari wadda ba ta zo da rai ba, da na kammala na nemi aiki sosai a matakin jiha ban samu ba.
A lokacin da aikin kidaya ya bijiro, sai hukumar ta nemi ma’aikata sosai, a wannan lokacin ne na samu shiga da aka kammala aikin a shekarar 1991 na ci gaba da aikin na dindindin da su har zuwa shekarar 2010. Daga nan na jingine aikin na koma harkar kungiyoyi masu zaman kansu na duniya kan ayyukan kananan hukumomi har na zama shugabar kula da ayyukkansu tare da ma’aikata 14 karkashina muna aiki har tsawon shekara hudu. Da na ga na yi shekaru da yawa bana wurin aiki sai na dawo ko ba kamai na kusa samun girma a mataki na 16 bayan na ci jarrabawar karin girman, sai ga wata sanarwa daga Asusun Kula da kananan Yara wato UNICEF na neman ma’aikata na cika fom na samu na nemi damar tafiya a ma’aikatarmu aka aka ba ni damar tafiya har yanzu ina aiki da su a matsayin shugabar sashen ilimi, na kammala karatun digirina na biyu a Jami’ar Usman danfodiyo.
kasashen da na taba ziyarta
Kenya ce kasar da na fara zuwa a lokacin da na kafa tawa kungiyar taimakon al’umma aka fito da wani fom don tafiya bita tsawon mako uku kan gabobin mata na haihuwa da hanyoyin kare kai a shekarar 2004. Har ila yau, a shekarar 2005 na koma Sudan wurin bitar kwana 11 kan matsayin mata a Musulunci, bayan na dawo a shekarar 2005 na tafi kasar Malawi, UNPA suka zabe mu mu wakilci Najeriya a taron kasashe 45 a shekarar 2006 na tafi Masar kan wani taro mako guda, na koma a shekarar 2007 na yi mako uku in da muka duba matsayin Musulunci kan tsarin haihuwa. A shekarar 2008 na tafi Amurka na yi mako uku, inda na ziyarci jihohinsu guda bakwai. Daga nan na ziyarci Saudiyya da birnin Dubai da kuma kasar Afirka ta Kudu.
kalubale
Cikas na farko dana samu wurin haihuwa tun da nake ban taba haihuwa da kaina ba, sai dai a yi mini fida a cire kan haka da zaran na ji alamun haihuwa nakan je a ciremin tun kafin lokacin nakuda, reno shi ma don kusan ni kadai ce can da nan, maigidana ba ya zama kan harkokin aikinsa musamman kungiyar malaman jami’a tafiyarsa tafi zamansa yawa.
Iyali
Allah ya albarkacemu da yara uku mata guda tana karatu a Jami’ar Bayero ta Kano, guda tana aiki, dayar kuma tana karatu a Jami’ar danfodiyo a shekarar karshe.
Burina a lokacin kuruciyata
Duk da cewa buri ba ya karewa, Allah Ya cika mini mafi yawansu kamar na ba zan yi aure ba har sai na kammala karatun jami’a, na samu mijin da zai barni na yi abin da nake so mutukar bai saba wa addini da al’ada ba, kasashen da nake jinsu nake son zuwa ban da Spain da Italiya da Aljeriya dukansu na kai ziyara.
Abin da take son a tuna ni da shi
Wani abin ba ka sani ba ka yi, amma wanda na sani nake so a tunani da shi bai wuce taimakon da muke yi wa yara mata wajen samar musu da sana’ar dogaro da tallafi don kyautata rayuwarsu. Mun yi shekaru muna yi da fatan ya yi tasiri ga rayuwar al’umma da fatar za a tuna da gudunmuwar bayan ba na nan.
Shawarata ga ’yan mata
Akwai gyara babba don mu iyayen yanzu muna da sakaci, da mun yi yadda mahaifanmu suka yi mana tarbiya da abin bai zama haka ba. Duba yadda ake bari diya mace ta yi nisa da gida ko aganta da wani abu ba za a binciketa inda ta samu da wanda ya ba ta da dalilin ba ta abin ba, mace ta je talla ba wani yaro ko tsohuwa tare da ita ta bar unguwa da kofar gidansu ba gudun ta samu wani abin magana, ko tarbiyyarta ta susuce. Yanzu za ka ga uwaye na korar diyansu ba sa son sanyasu a jiki sabanin in da aka fito.
Ra’ayina game da makarantu ’ya’ya mata
Kwalliya ba ta biya kudin sabulu, akwai sauran rina a kaba akwai yaran da ya kamata akai su makaranta ba a kaisu ba har yanzu muna yaki da yekuwa don a gane akwai wayewa fahimta ce babu don ana ganin amfanin bokon, amma an ki sanyasu.
Abin da ba zan manta da shi ba
diyata da na rayu da ita wata tara a cikina ta fito babu rai, a lokacin bana cikin hayacina ban taba ko ganinta ba har binneta.
Shawarata ga iyaye mata
Mata mu tashi tsaye mu kula da tarbiyyar yara. Aure yana shiga cikin wani hali, zarge-zarge na yawaita a daina don yafi yawa wajen mata nasiha wurin miji yafi zargi da habaici, makaratar farko a wajen mata uwa ce. Mu zauna mu kula da yaranmu da dabi’unsu da abokan huldarsu don guje masu daukar halin banza, mu kula da matanmu sosai don gudun shiga wani halin da baki sani ba, saboda fyade na yawaita kada a yi wa ’yarki lahani baki sani ba har abu ya baci, ku rika hulda da ’ya’yanku don sanin rayuwarsu da farin cikinsu da bakincikinsu.