Iyaye na ba da gudunmawa wajen lalacewar matasa – Galadiman Bauchi
Galadiman Bauchi kuma Hakimin Zungur da ke Jihar Bauchi Alhaji Sa’idu Ibrahim Jahun ya bayyana damuwarsa kan yadda wasu daga cikin iyaye suka kasa sauke nauyin da ke kansu na ba da tarbiyya ga ’ya’yansu, inda ya ce babu wata al’umma da za ta samu ci gaba mai amfani sai tana da matasa masu ilimi […]
Galadiman Bauchi kuma Hakimin Zungur da ke Jihar Bauchi Alhaji Sa’idu Ibrahim Jahun ya bayyana damuwarsa kan yadda wasu daga cikin iyaye suka kasa sauke nauyin da ke kansu na ba da tarbiyya ga ’ya’yansu, inda ya ce babu wata al’umma da za ta samu ci gaba mai amfani sai tana da matasa masu ilimi da sanin ya kamata.
Galadiman Bauchin ya bayyana haka ne lokacin da yake tattaunawa da wakilinmu a a garin Bauchi, a farkon wannan mako, inda ya ce Allah zai tambayi kowa game da yadda ya yi tarbiyyar ’ya’yansa a gobe kiyama don haka ya kamata al’umma da sauran masu ruwa da tsaki su ba da tasu gudunmawa domin farfado da tarbiyyar matasan.
Galadima ya ce akwai dimbin matasa a Bauchi da suke ta’ammali da miyagun kwayoyi, kuma a matsayinsu na sarakuna, za su ci gaba da ba da tasu gudunmawa ta wajen wayar da kan matasan illolin da ke tare da shan miyagun kwayoyi.
Ya ce, a shekarun baya da wahala mutum ya ga matashi yana zaman kashe wando ko yawon roko a tsakanin al’umma, amma a yanzu lamarin ya canja sakamakon yadda wasu daga cikin iyaye suka koma suna bauta wa ’ya’yansu, maimakon dora su a kan turba tagari.