Iyaye su tallafa wa yara su koyi sana’o’in hannu -Musa Alburhan
Shugaban majalisar malamai na kungiyar Izalatul bid’a wa ikamatus sunna, reshen ’yan kwaba da ke karamar Hukumar Jos ta Arewa a Jihar Filato, Ustaz Musa Salihu Alburhan ya bukaci iyaye su rika tallafa wa ’ya’yansu wajen ganin sun koyi sana’o’in hannu don su dogara da kansu. Ustaz Musa Alburhan ya bayyana wannan bukata ce a […]
Shugaban majalisar malamai na kungiyar Izalatul bid’a wa ikamatus sunna, reshen ’yan kwaba da ke karamar Hukumar Jos ta Arewa a Jihar Filato, Ustaz Musa Salihu Alburhan ya bukaci iyaye su rika tallafa wa ’ya’yansu wajen ganin sun koyi sana’o’in hannu don su dogara da kansu.
Ustaz Musa Alburhan ya bayyana wannan bukata ce a lokacin da yake jawabi a wajen bude wata makarantar koyon kwamfuta mai suna Sahlan Integrated Systems da aka gudanar a garin Jos.
Ya ce yanzu a Nijeriya shugabanni ba su damu da talakawa ba wajen samar musu da ayyukan yi. Don haka ya zama wajibi iyaye, bayan sun sanya ’ya’yansu a makaranta kuma su sanya su a wajen koyan sana’ar hannu, domin su samu abin da za su dogara da kansu. Ya ce idan yaro ya doraga da karatu kawai, to zai gama makaranta ya zo babu aikin yi.
Ya ce don haka bude wannan makaranta ta koyon ilmin kwamfuta yana da matukar amfani ga al’umma. Ya ce babu shakka Allah ne kadai ya san yawan wadanda za su amfana da wannan makaranta. Domin a halin da ake ciki ilmin kwamfuta shi ne gaba a duniya. Ya ce wajibi ne dukkan mutumin da yake son ya tafi da zamani ya karanci ilmin kwamfuta.
A nasa jawabin, shugaban makarantar, Malam Muhammad Shafi’u Yakubu ya bayyana cewa an bude wannan makaranta mai suna Sahlan ne domin magance kalubalen da al’ummar musulmi suke fuskanta kan ilmin na’urar kwamfuta.
Ya ce wannan makaranta za ta rika karantar da yara da manya da dukkan wadanda suke bukatar su koyi ilmin kwamfuta.
Ya ce tun kafin su bude wannan makaranta sun sami nasarar fito da wata jaridar Hausa mai suna Sahlan, wadda take fitowa a duk mako uku. Ya ce tun da suka fara buga wannan jarida ba su taba yin fashi ba.