Iyaye sun haifi yaran da suka fi su ‘siffar tsufa’

Rahoton yaran, ’yan asalin kasar Indiya ya dau hankali a kafafen yada labarai.

Iyaye sun haifi yaran da suka fi su ‘siffar tsufa’

Yaran da aka haifa da cutar tsufan a Indiya

Wasu yara biyu ’yan uwan juna masu suna Keshab da Anjali Kumar, daga Jihar Jharkhand a Indiya da suke fama da wasu nau’ukan cututtuka biyu da aka fi sani da Cutis Lada da Progeria, wanda ke sa fatar jikinsu ta yi kamanni da ta tsofaffi duk da karancin shekarunsu.

Rahoton yaron da ’yar uwarsa ’yan asalin kasar Indiya sun dau hankalin jama’a a kafafen yada labarai a matsayin, “yara da aka haifa da siffar jikin tsofaffi, amma da shekarun yara” a shekarar 2016.

A lokacin Anjali tana da shekara 7 kuma kanin nata yana da watanni 18 kacal, amma dukkansu sun riga sun yi kama da wadanda suka kai shekara 80 zuwa 89.

Kuma ba wai yankwanewar fatarsu ba ne kawai, wanda ba a saba gani ba, suna fama da ciwon gabobi jiki irin na tsofaffi.

Wannan halin da ake ciki ya sa aka yi musu lakabi da ‘Benjamin Button siblings,’ (Yara ’yan uwa da aka haifa da tsufansu) kadan daga cikin yanayin halin da yaran ke fuskanta a cikin dan gajeren labari na F. Scott Fitzgerald.

Keshab da Anjali Kumar an gano suna da cutuka biyu progeria da cutis lada, yanayi biyu na musamman da ba kasafai ake samun mutum da su ba.

Abin takaicin shi ne ba za su iya warkewa ba. An haife su a Ranchi, Babban Birnin Jihar Jharkhand ta Indiya, Keshab da Anjali ba kawai suna fuskantar ciwon gabobi ba ne, wanda yake da ya yi sanadiyyar yadda aka haife su ba, har ma da cin zarafi da yara wadanda ke kiransu da kowane nau’i na lakabin suna, suna yi masu dariya idan sun shiga cikin jama’a.

Abin bakin ciki shi ne, akwai abubuwa da yawa da iyayensu da ’yar’uwarsu da za su iya yi don taimakawa, amma sai kalilan ne za su iya.

“Yaran idan sun je makaranta ana kiransu da sunaye kamar daadi (wato kaka) ko budhiya (tsohuwar budurwa), ko bandariya (biri) ko hanuman (ubangijin biran Hindu), wanda hakan yana ba ni haushi,” inji Anjali a wata tattaunawarta da manema labarai.

A cikin 2016, an ba da rahoton cewa, iyayen yaran wato Shatrughan Rajak da Rinki Debi, sun yi fatan za su yi wa ’ya’yansu abubuwa da yawa, amma likitoci sun gaya musu cewa, babu yadda za a yi a taimaka musu a Indiya, kuma ko a kasashen waje hanya daya ce kawai, sai dai a ba su maganin rage radadin zafin ciwon.

Iyayen ba su gamsu sosai ba, saboda ba za su iya mallakar maganin ba, an yi wa yaran biyu maganin wanda ba shi da tasiri mai yawa.

Dukkan cutukan biyu suna da alamun da suka fi zurfin fata, kuma masu fama da cutar gaba daya suna da karancin matakan riga-kafi kuma sun kasance cikin cututtuka masu hadari idan an kamu, kamar cututtukan kirji har ma da bugun zuciya.

An yi sa’a, abubuwa sun canza ga Keshab da Anjali tun lokacin da kafofin labarai suka fara ba da labarinsu, kusan shekara shida da suka wuce.

Bayan wallafa hotunan yaran da jikin tsofaffi aka yi ta yada su a yanar gizo, wata kungiya mai zaman kanta mai suna Care Today Fund ta tuntubi iyayen yaran tare da ba su tallafin jinya.

Anjali da Keshab tun daga lokacin an yi musu gyaran fuska don rage yankwanewar fatar jikinsu kuma sun yi kyau fiye da yadda suke yi a shekarar 2016.

Tashar Truly’s Born Different a kwanan nan ta wallafa wani bidiyo a YouTube a kan Keshab da Anjali Kumar, kuma sun ba da rahoton cewa, su biyun ba sa rabuwa da juna kuma suna goyon bayan juna don shawo kan matsalolin da suke fuskanta kowace rana.