Iyaye sun kashe dansu da guba kan zargin maita

Su da kansu suka hada gubar suka yaudari dansu ya sha, ya mutu.

Iyaye sun kashe dansu da guba kan zargin maita

Jami’an ‘Yan sanda

Wasu iyaye sun shiga hannu bayan sun ba wa dansu mai shekara 10 guba ya mutu, kan zargin sa da maita.

Magidancin da matarsa sun yaudari yaron ne suka ba shi gubar bayan ’yan tsubbu sun ce musu yana da maita, abin da iyayen ke zargin shi ne ya sa suke fama da talauci da rashin lafiya da rashin sa’a da kuma rashin kwazon ’yan uwan yaron a makaranta.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Anambra ta ce iyayen yaron ne da kansu suka hada gubar suka ba shi, bayan sun yaudare shi cewa magani ne da zai cire masa maitar.

Kakakin Rundunar, SP Odiko Macdon, ya shaida wa wani taron ’yan jarida a ranar Talata cewa iyayen yaron sun amsa cewa su ne suka ba shi gubar, da kuma dalilinsu na yin hakan.

“Ranar 29 ga Agusta, 2021 muka samu rahoto daga kauyen Ekpat Iduot cewa wani magidanci da matarsa sun hada baki sun ba dansu guba sun kashe shi saboda zargin sa da maita.

“’Yan sanda masu binciken kwakwaf sun je sun cafko ma’auratan, wato mahaifin yaron da matarsa.

“Da aka titsiye su, sun amsa cewa su ne suka hada wata guba da ake kira ‘Evil Beans’ suka ba shi da sunan za su cire masa maita.

“A cewarsu, dubar da aka yi musu ta nuna cewa shi ne dalilin taulauci da rashin lafiya da rashin sa’ar da suke fama da su, gami da rashin kokarin ’yan uwansa na wurin uba a makaranta.

“A binciken da muka gudanar a gidan mun gano wani bango da matar mahaifin yaron ta rubuta cewa shi ne maye a gidan.

“An riga an dauki hotuna sannan aka wuce da gawar zuwa dakin ajiyar gawa domin gudanar da bincike,” inji shi.