Iyaye sun maka dansu a kotu saboda rashin haifa musu jika
Mahaifan matukin jirign saman suna neman ya biya su diyyar Naira miliyan 270 ko ya haifa musu jika cikin wata shida.
Wasu iyaye sun maka dansu a kotu suna neman ya biya su diyyar Naira miliyan 270 saboda rashin haifa musu jika.
Ma’auratan da ke zaune a Jihar Uttarakhand da ke Arewacin kasar Indiya, sun yi karar dansu Shrey Sagar mai shekara 35, wanda shi kadai suka haifa, suna neman diyya ne bayan ya shekara shida da aure amma har yanzu bai haifa musu jika ba.
- An kama Kansila mai ci da AK-47 kusa da sansanin masu garkuwa da mutane
- Dalibai sun kashe matashiya a Sakkwato saboda zargin batanci ga Annabi
Don haka suke neman dan nasu, wanda matukin jirgin sama ne, ya biya su diyyar Dala 650,000, kimanin Naira miliyan 270, idan har bai haifa musu jika ba kafin karshen shekarar da muke ciki ba.
Mahaifinsa, Sanjeev mai shekara 61 tare da matarsa, Sadhana Prasad, mai shekara 57, sun shaida wa kotu cewa sun kashe duk kudin da suka tara wajen tarbiyyarsa da tura shi makarantar koyon tukin jirgin sama a Amurka, da kuma shirya mishi kasaitaccen bikin daurin aure.
Don haka suke neman diyyar kimanin Dala 650,000 (kimanin Naira miliyan 270) daga wurinsa idan har shekarar ta kare bai haifa musu jika ba, cikin wata shida masu zuwa.
Maihaifin ya bayyana cewa sun kashe kimanin Dala 65,000 (kimanin Nira miliyan 26) wajen tura dan nasu makarantar koyon tukin jirgi a kasar Amurka a shekarar 2006.
Bugu da kari, sun kashe kusan Dala 80,000 (kimanin Naira miliyan 33) wajen shirya bikin auren dan nasu a wani otal din alfarma.
A shekarar 2016 ne mahaifansa suka shirya bikin aurensa da matarsa, Shubhangi Sinha, mai shekara 31 a yanzu, da fatan za su haifa musu jika, ba ruwansu da jinsi, “wanda da za su rika wasa da shi” bayan sun yi ritaya daga aiki.
Sai dai kuma shekara shida baya auren, har yanzu dan nasu da surukar tasu ba su haihu ba.
Mahaifin wanda ake karar, ta bakin lauyansu, ya ce, “Burin iyaye shi ne su zama kakanni; Amma sai jira suke ta yi na tsawon shekaru, su ga su ma sun yi jika.”
Kawo yanzu dai, wadanda ake kara ba su ce komai ba tukuna.