Iyaye sun yi karar saurayin ’yarsu kan fasa auren ta
An gurfanar da shi a gaban kotu bisa zargin bata wa budurwa lokaci
Iyayen wata budurwa sun gurfanar da wani saurayinta gaban Kotun Shari’ar Musulunci ta Uku da ke Kofar Kudu a Kano bisa fasa aurenta da ya yi inda suke zarginsa da bata mata lokaci tare da janyo musu asarar kashe kudin da suka yi.
Iyayen budurwar mai suna Hafsa Bashir sun shaida wa kotun cewa bayan da saurayin ’yarsu ya nemi auren ta har aka kai kayan lefe daga baya ya bayyana cewa ya fasa auren ta ba tare da wani dalili ba.
- An dana kanin Kwankwaso sarautar Makaman Karaye
- Kannywood ta zama kasuwar bukata – Zango
- An kai daraktan Kannywood Ashiru Nagoma asibiti
- Dalilin da ya sa na bude gidan abinci- Fati Bararoji
Malam Bashir Dandago ya bayyana wa kotun cewa bayan sun kammala komai game da shirin biki har da sayen kayan daki da abincin biki, sai saurayin ya ce ya fasa auren ’yarsu tare da neman a mayar masa da dukkan kayansa.
A cewar Malam Bashir Dandago, da suka nemi ya sanar da su dalilinsa na fasa auren, sai ya gaza bayar da wata gamsasshiyar amsa inda ya ce shi kawai kayansa yake bukata.
“Muna rokon wannan kotu mai adalci ta bi wa yarinya hakkinta na bata mata lokaci da aka yi tare da sanya ta cikin damuwa da saurayin ya yi.
“Yaya za a yi a makon biki an gama komai har da kayan daki an saya, an yi abincin biki sai kawai ya zo ya ce ya fasa aure? Wannan ba daidai ba ne,” inji shi.
Sai dai a zaman kotun, saurayin ya bayyana wa kotu cewa wacce ta yi dalilin auren mai suna Hajiya Asabe ce ta gindaya masa sharudda wadanda shi kuma ya ga ba zai iya bin su ba don haka ya fasa yin auren.
A cewarsa mai dalilin auren ta bayyana masa cewa dole ya kama babban wurin da za a yi biki tare da fitowa ya yi rawa da matarsa a wajen bikin, abubuwan da ya ce ba zai iya aikatawa ba saboda gudun zubewar mutuncinsa a idanun jama’a.
Sai dai Hajiya Asabe ta musanta da’awar saurayin inda ta ce “Gaskiya ban san wannan magana ba, ba a yi ta ba, a takaice dai kirkirarta ya yi don ya nemi mafaka.
“Ni dai lokacin da ya ce ya fasa auren na nemi jin dalili, amma ya ce shi dai kawai ya fasa auren amma bai gaya min dalili ba.
“A lokacin har na nemi ya ba yarinyar wasu daga cikin kayan lefen amma ya ki amincewa,” inji ta.
Alkalin Kotun Mai shari’a Halhalatul Huza’i Zakariyya Aliyu ya dage shari’ar zuwa ranar 15 ga watan Fabrairu don ci gaba da bin bahasi.