Iyayen Amarya sun ki karbar tsoffin kudi a matsayin sadakin ’yarsu a Neja
Sun ce ba sa bukatar kashe kudi a lokacin, kuma ba su da asusun ajiyar a banki
Iyayen wata budurwa da ke Karamar Hukumar Gbako ta Jihar Neja, sun bukaci waliyyan angon da za daura aurensa da ’yarsu da su mayar da takardun N1,000 da na N5,000 din da suka kai a matsayin kudin sadaki.
Aminiya ta gano cewa iyayen angon dai sun kai kudaden da ba a bayyana adadinsu ba a matsayin na sadaki da na sauran saye-saye a shirye-shiryen bikin.
- NAJERIYA A YAU: Kalubalen da muke fuskanta a harkar sufuri – ’Yan Najeriya
- ’Yan sanda sun kama magoya bayan Arsenal kan murnar doke United
Kodayake ba a dage bikin ba, amma iyayen amaryar sun yi korafin cewa ba su da bukatar kashe duka kudaden kafin nan da ranar 31 ga watan Janairu, wa’adin da CBN ya bayar ba daina amfani da su, sannan ba su da asusun bankin da za su zuba su a ciki.
Hakan ne ya sa suka ki karbar tsoffin kudaden, tare da bukatar a ba su sababbi matukar ana son a daura auren.
Wani dan uwan angon ya yi bayanin cewa, “Mun kai kudaden gidan amaryar da dan uwanmu yake shirin aura, amma sai suka kira ni ranar Lahadi suka ce mu zo mu karbi kudaden har sai mun sami sabbin takardun kudaden ma kawo.
“Sun ce ba su da inda za su kai tsoffin, saboda haka za mu mayar har sai mun sami sabbin,” in ji shi.
Ya kuma ce mutane da dama na dari-darin karbar kudaden a yankin saboda fargabar ba za su iya kashe su kafin cikar wa’adin na CBN ba.
Aminiya ta gano cewa tuni wasu ’yan kasuwa a wasu kauyukan Jihar ta Neja suka fara daina karbar tsoffin kudaden ko kuma su dakatar da kasuwancin nasu a daidai lokacin da har yanzu bankuna ke ci gaba da bayar da tsoffin kudaden.
Da wakilinmu ya zagaya wasu kauyuka da kananan garuruwa na Jihar, ya gano cewa galibinsu ba su ma da bankuna.