Iyayen daliban Najeriya na tunanin mayar da su Port Sudan bayan Masar ta rufe iyakarta

Kwana uku da isar daliban kan iyaka, amma gwamnatin Masar ta hana su shiga cikin kasarta.

Iyayen daliban Najeriya na tunanin mayar da su Port Sudan bayan Masar ta rufe iyakarta

Iyayen daliban Najeriya da suka makale a iyakar kasar Masar bayan sun bar kasar Sudan mai fama da yaki, sun fara tunanin ’ya’yan nasu su koma birnin Port Sudan na kasar, ko za su samu jirgi zuwa Najeriya.

Duk da yakin da ake fama da shi a kasar ta Sudan, kawo yanzu dai ana ci gaba da zirga-zirgar jiragen sama a birnin Port Sudan, duk da cewa an rufe sararin samaniya a wasu sassan kasar.

Iyayen daliban da suka kwana uku a kan iyakar kasar Masar ba tare da kasar ta ba su izinin shiga ba saboda rashin takardu, bayan sun baro Sudan saboda yaki, na ganin maimakon jiran gawon shanu, gara su nema wa ’ya’yan nasu mafita ta Port Sudan.

Suna tunanin cewa a Port Sudan, wanda yankin kasar Sudan ne za a samu jirgin da zai kwaso ’yan Najeriya zuwa gida, ga shi babu bukatar takardun neman izinin da suka hana su tsallakawa zuwa kasar Masar, inda gwamnati ta tsara za su hau jirgi zuwa gida.

Gwamnatin Najeriya ta shirya kwashe ’yan kasar wadanda yaki ya ritsa da su a Sudan a motoci zuwa birnin Alkahira na kasar Masar, inda daga nan za a dauke su a jirgi zuwa gida.

Sai dai tun ranar Alhamis rukunin farko na ’yan Najeriyar da aka kwaso daga Khartoum, fadar kasar Sudan suka isa iyakar kasar Masar da ke Aswan, amma hukumomi sun hana su izinin tsallakawa saboda rashin takardun da ya kamata.

Daliban da sauran ’yan Najeriyan da Ofishin Jakadancin Najeriya da ke Khartoum ya kwaso, sun zargi jami’an ofishin da rashin yin abin da ya kamata domin sama musu izinin shiga kasar Masar.

Daya daga cikin iyayen daliban ta yi ikirarin yin magana da Jakadan Najeriya da ke Alkahira, kuma ya tabbatar mata cewa hukumomin kasar Masar ba su ba da izinin shiga kasar ga ’yan Najeriyan da aka kwaso daga Sudan mai fama da yaki ba.

Ganin cewa, tun da har yanzu jirage na tashi a Port Sudan, iyayen daliban ke ganin babu amfanin jiran tsammani a kan iyakar kasashen biyu.

Hasali ma, idan sauran ’yan Najeriya da suka baro Khartoum ranar Juma’a suka isa kan iyakar na Masar da ke Aswan, abun zai kara rincabewa.

Don haka suke ganin mafita ita ce komawar rukunin farko na matafiyan Port Sudan, watakila daga nan za a samu jirgi ya dauko su kai-tsaye zuwa Abuja.

A ranar Juma’a dai bangarorin da ke yaki da juna a Sudan sun amince su tsawaia wa’adin da suka bayar na tsagaita wuta da kwana uku, domin ba da damar aiwatar da ayyukan jinkai da kuma kwashe ’yan kasashen waje daga kasar.

A ranar Lahadi dai wa’adin yake karewa, ko da yake tun ranar Juma’a da aka tsawaita wa’adin an yi ta gwabza yaki tsakanin sojojin gwamnati da kuma bangaren mayakan sa-kai na RSF a sassan Khartoum da wasu yankunan kasar.

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno