Iyayen jami’an SSS da aka kashe a Nasarawa sun ce ba su yafe ba
Iyayen jami’an tsaron kasa na SSS goma da aka kashe a harin ’yan kungiyar matsafa ta Ombatse a Jihar Nasarawa kusan wata uku da suka gabata sun gudanar da zanga-zanga lokacin ziyarar Mataimakin Shugaban kasa Muhammad Namadi Sambo, inda suka nemi a hukunta makasan tare da bayyana cewa ba za su yafe ba.Jim kadan da […]
Iyayen jami’an tsaron kasa na SSS goma da aka kashe a harin ’yan kungiyar matsafa ta Ombatse a Jihar Nasarawa kusan wata uku da suka gabata sun gudanar da zanga-zanga lokacin ziyarar Mataimakin Shugaban kasa Muhammad Namadi Sambo, inda suka nemi a hukunta makasan tare da bayyana cewa ba za su yafe ba.
Jim kadan da kashe jami’an tsaron a kauyen Alakyo da ke kusa da Lafiya a ranar 7 ga Mayun da ya gabata, Darakta Janar na Hukumar SSS, Ita Ekpenyong ya bayyana cewa hukumar ta yafe wa makasan jami’an SSS din goma.
Sai dai iyayen jami’an dauke da kwalayen da aka yi rubuce-rubuce a kansu sun fadi a ranar Litinin da ta gabata cewa ba za su yafe wa kungiyar Ombatse ba.
Tun misalin karfe 9:00 na safe masu zanga-zangar suka taru a harabar ginin Babbar Kotun Tarayya da Mataimakin Shugaban kasa ya bude, inda suka yi sahu a kan hanyar da ayarinsa za su bi zuwa harabar kotun.
Sambo wanda ya isa wurin tare da Gwamna Umaru Tanko Al-Makura da Ministan Watsa Labarai Labaran Maku, wanda dan jihar ne, sun samu tarba daga masu zanga-zangar da suke rera cewa: “Muna bukatar adalci, muna so a yi wa ’ya’yanmu adalci.”
Sai dai jami’an tsaro sun hana masu zanga-zangar zuwa kusa da ginin kotun har aka kammala bikin. An gudanar da bude ginin ba tare da wata matsala ba, inda Mataimakin Shugaban kasa ya bar wurin da misalin karfe 12:21 ya sake wuce masu zanga-zangar.
Kwalayen suna dauke da sakonnin da ke cewa: ‘Ka taimaka Shugaban kasa, Muna bukatar ’ya’yanmu da aka kashe,’ ‘Muna cike da bakin ciki, Shugaban kasa don Allah ka sanya baki,’ da kuma ‘Abin da muke cewa, mako 12 ke nan da faruwar lamarin.’
Da suke tattaunawa da Aminiya, masu zanga-zangar wadanda galibinsu tsofaffi ne sun koka kan abin da suka kira rashin katabus din Gwamnatin Tarayya game da kashe ’ya’yansu da ’yan Ombatse suka yi.
Sun ce sun kadu da gwamnati ta ki cewa komai ko daukar wani mataki don nuna damuwa ga iyaye da iyalan jami’an SSS din da aka kashe.
Dokta Nandul Durfa, mai shekara 64, kuma mahaifin ma’aikacin SSS, Timman Durfa, da ya jagoranci zanga-zangar ya shaida wa Aminiya cewa, sun tattaro juna ne ta hanyar waya suka hadu a Lafiya ranar Lahadi don amincewa da abin da za su rubuta a kwalayen. Ya ce ya kira sauran iyaye da suka hada da Madaki Damian daga Abuja da Nimsel Nanyal daga Jos don shiga zanga-zangar. Sai su kuma suka kira Sa’idu Isah Gobir wanda ya zo daga Awe a Nasarawa da Madam Misis Godiya Makama daga Nasarawa-Toto. Mun kai kimanin mutum 17 ciki har da wakilan wasu iyaye.”