Iyayen mannannun tagwaye sun yaba wa Sarkin Saudiyya
Iyayen wasu ’yan tagwaye sun yaba wa Sarki Abdullah na Saudiyya sakamakon wani aikin raba ’ya’yansun da aka gudanar cikin nasara bayan da aka haife su a manne. Sarkin ya ba da umarnin gudanar da aikin raba su ne kyauta a wani asibitin tunawa da Sarki Abdul’aziz da ke birnin Riyadh.Likitoti sun kwashe sa’a shida […]
Iyayen wasu ’yan tagwaye sun yaba wa Sarki Abdullah na Saudiyya sakamakon wani aikin raba ’ya’yansun da aka gudanar cikin nasara bayan da aka haife su a manne.
Sarkin ya ba da umarnin gudanar da aikin raba su ne kyauta a wani asibitin tunawa da Sarki Abdul’aziz da ke birnin Riyadh.
Likitoti sun kwashe sa’a shida da minti 40 a aikin raba ’yan tagwayen, wanda aka gudanar har sau shida a jere. ’Yan tagwayen, wadanda ke da sunayen Christ da Christian Kritoci ’yan asalin kasar Iraki ne da aka haife su watanni uku da suka wuce a manne daga gefen kirjinsu. Kafar yada labarai ta ‘Arab News’ ta tabbatar da cewa suna ci gaba da murmurewa a gadon asibiti.
Wannan ba shi ne karo na farko da Sarki Abdullah yake daukar nauyin aikin raba ’yan tagwayen da aka haife su a manne ba. A baya ma ya dauki nauyin aikin raba wasu tagwayen da dama ciki har da wasu da suka fito daga kasashen Sudan da Yemen da Masar da Malaysia da Philippines da Poland da Moroko da kuma Iraki.