Iyayen Mary Habila sun ce a ba su gawarta don binne ta
Lauyan iyalan, Kaile Adamu Yusuf ya ce iyayen ba su amince a yi mata gwajin gano musabbabin mutuwarta ba, saboda dalilan addini da al’ada.
Iyayen marigayiya Mary Habila, wata ma’aikaciyar jinya mai shekara 26 da aka tsinci gawarta a gidan hutun Ministan Ayyuka, David Umahi sun miƙa ƙorafi ga Sufeto Janar na ’Yan Sandan Najeriya, Olatunji Disu.
Inda suka nemi a miƙa masu gawarta domin binne ta.
- INEC na nazarin gwajin zaɓen shugaban ƙasa kafin 2027
- Sabon hari: An kashe shanu da raunata wasu a Filato
Lauyan iyalan, Kaile Adamu Yusuf ya ce iyayen ba su amince a yi mata gwajin gano musabbabin mutuwarta ba, saboda dalilan addini da al’ada.
Ya kuma zargi rundunar ’yan sandan Jihar Ebonyi da ci gaba da riƙe gawar duk da buƙatar da iyalan suka yi na karɓarta.
Ya ce, marigayiyar ma’aikaciyar jinya ce, ba likitar motsa jiki ba, kamar yadda wasu ke yaɗa wa, kuma ta yi kusan shekara uku tana aiki tare da Ministan Ayyuka bayan an tura ta daga Jami’ar Kimiyyar Lafiya ta David Umahi.
A nasa ɓangaren, mahaifinta Tanko Habila Wisdom ya ce iyalan ba su zargi kowa da hannu a mutuwarta ba, yana mai roƙon ’yan sanda su mutunta buƙatarsu na karɓar gawar domin binne ta cikin girmamawa.
Ya kuma yi kira da kada a mayar da mutuwar ’yarsa batun siyasa.