Iyayen matashin da aka harbe a zanga-zangar Kano na neman adalci

Yayar matsahin ta ce, “Zanga-zanga kawai suke yi, amma aka ce ’yan daba ne [aka bude musu wuta]. Shin talaka ba shi da ’yancin neman haƙƙinsa ne?”

Iyayen matashin da aka harbe a zanga-zangar Kano na neman adalci

Wasu matasan Najeriya a lokacin wata zanga-zanga a kan titin Legas-Ibasan kan cin zalinsu da ‘yan sanda ke yi. (Hoto:PIUS UTOMI EKPEI / AFP) (Photo by PIUS UTOMI EKPEI/AFP via Getty Images)

Iyayen wani matashi ɗan shekara 25 wanda ake zargin ’yan sanda sun harbe shi har lahira a yayin zanga-zangar tsadar rayuwa a Jihar Kano suna neman a bi masa haƙƙinsa.

Aƙalla mutane takwas ne ake zargin ’yan sanda sun harbe har lahira a lokacin da aka yi arangama tsakaninsu da masu zanga-zangar a unguwar Rijiyar Lemo da ke Ƙaramar Hukumar Fagge.

Bashi Muhammad na daga cikin matasan da suka gamu da ajalinsu a wannan waƙi’a da ta auku a kan Babba Titin Kastina da ke yankin.

Iyayen Bashir sun bayyana cewa jami’an tsaron sun hallaka shi ne a yayin da yake neman haƙƙinsa da dokar ƙasa ta ba shi a matsayinsa ba ɗan Najeriya.

Mahaifinsa, Malam Muhammad Lawal, ya ce an harbe Bashir ne kimanin mintoci 15 da fitowarsa daga gida domin halartar zanga-zangar.

Ya bayyana cewa matasa maza da mata da dama ne suka fita zanga-zangar da aka kashe dansa a wannan rana.

“Yana tare da sauran mutane da suka fita zanga-zangar lumana ɗauke da kwalaye

“Wajen Azahar jami’an tsaro suka iso wurin, masu zanga-zanga na ihu ‘bama yi, bama yi’ shi ne jami’an tsaro suka buɗe musu wuta suka harbe dana,” in ji mahaifin Bashir.

Wasu danginsa sun yi zargin cewa ’yan sanda sun yi amfani da harsashi mai rai a kan masu zanga-zangar da suka yi musu ihu.

Yayar marigayi Bashir mai suna Khadija, ta ce, harsashi ya same shi ne a lokacin da yake ƙoƙarin tserewa domin ya ɓoye.

“Zanga-zanga kawai suke yi, amma aka yi musu sharri cewa ’yan daba ne [aka bude musu wuta]. Shin talaka ba shi da ’yancin neman haƙƙinsa ne?

“Don haka muna neman a bi masa haƙƙinsa,” in ji Khadija cikin juyayi.

A halin da ake ciki, Gwamnatin Kano ta sassauta dokar hana zirga-zirga ta awa 24bd ta sanya zuwa awa 18.

Sai dai duk da haka yawancin ’yan kasuwa ba su bude shagunansu ba a ranar Litinin.

A ranar ce kuma aka gudanar da salloli da addu’o’in na musamman domin neman sauƙin rayuwa a sassan jihar.

Kazalika masu zanga-zanga sun fita kan titunan Kano ɗauke da tutar kasar Rasha.

Rundunar ’yan sanda ta sanar da kama aƙalla mutane kan yin zanga-zanga ɗauke da tutar Rasha.

Tuni dai Gwamnatin Rasha ta nesanta kanta da zanga-zangar da ke wakana a faɗin Najeriya.

’Yan sanda a Jihar Kano sun ce sun kama aƙalla mutane 632 kan lalatawa da sace-sacen kayan jama’a da na gwamnati a lokacin zanga-zanga.

DSS ta kama ’yan Boko Haram 10 a Osun

Mutum 60 sun mutu a fashewar tankar mai a Neja

Solskjaer ya zama sabon kocin Besiktas

Nijeriya ta zama abokiyar hulɗar ƙungiyar BRICS