Iyayen wanda ya rasu a hannun DSS na bukatar bincike
Iyayen Aliyu Bukhari dan shekara 25 sun bukaci a gudanar da binciken dalilin rasuwar dan su wanda suke zargin ya rasu ne a hannun hukumar tsaron farin kaya DSS a Sokoto . Rahoton dai na bayyana cewa, DSS sun tsare Bukhari a lokacin da yake zaune a shagonsa, saboda zargin hannunsa a yin garkuwa da wani […]
Iyayen Aliyu Bukhari dan shekara 25 sun bukaci a gudanar da binciken dalilin rasuwar dan su wanda suke zargin ya rasu ne a hannun hukumar tsaron farin kaya DSS a Sokoto .
Rahoton dai na bayyana cewa, DSS sun tsare Bukhari a lokacin da yake zaune a shagonsa, saboda zargin hannunsa a yin garkuwa da wani yaro mai shekara hudu Umar Bashir inda aka yi amfani naira dubu 150 a matsayin kudin fansa, kafin a saki yaron.
An yi amfani da layin sadarwa n Aliyu Bukhari wajen biyan kudin fansan.