Iyayen ’yan matan Chibok sun fara fitar da rai wajen gano ’ya’yansu

Iyayen ’yan matan Chibok sun ce sun fara fitar da rai wajen gano ’ya’yansu kwanaki 81 bayan an sace su.daya daga cikin iyayen ’yan matan Chibok mai suna Mista James Yama ya ce: “Ina da yakinin cewa har yanzu Gwamnatin Tarayya ba ta yarda an sace ’ya’yanmu masu daraja ba.”Mista Yama mazaunin kauyen Mbalala mai […]

Iyayen ’yan matan Chibok sun fara fitar da rai wajen gano ’ya’yansu
Iyayen ’yan matan Chibok sun fara fitar da rai wajen gano ’ya’yansu

Iyayen ’yan matan Chibok sun ce sun fara fitar da rai wajen gano ’ya’yansu kwanaki 81 bayan an sace su.
daya daga cikin iyayen ’yan matan Chibok mai suna Mista James Yama ya ce: “Ina da yakinin cewa har yanzu Gwamnatin Tarayya ba ta yarda an sace ’ya’yanmu masu daraja ba.”
Mista Yama mazaunin kauyen Mbalala mai nisan kilomita kadan da garin Chibok ya ce ’yarsa Jinkai ’yar shekara 19 na daya daga yara masu hazaka a cikin iyalinsa.
Ya ce: “A yanzu muna ta kirga kwanaki cikin mummunan bakin ciki da takaici, amma ga alama kirgen namu ba zai zo karshe ba.  Abin bakin ciki ne a ce wadansu da ke zama a Abuja da ’ya’yansu cikin farin ciki, ba tare da masaniyar mawuyacin halin da muke ciki ba. Ba su kuma damu da halin da muke ciki ba.”
Ya ce a iya saninsu babu wani matakin ceto ’ya’yansu da aka dauka, ko wadanda suka tsira ma su  ne suka kubutar da kansu, ba wai taimakon gwamnati ko jami’an tsaro ba.
Habu Balla, mazaunin kauyen Mbalala ya bukaci Gwamnati ta ceto ’ya’yansu da ke hannun ’yan Boko Haram.
Ya ce: “Akwai Musulmi da Kirista a Chibok, haka a sauran kauyukan da ke kusa da Chibok. Don haka a rika kallon abin fiye da yadda ake yi masa kallon addini ko yare ko kabila. Muna cikin fargaba a Mbalala, saboda babu wani abu mai kama da tsaro, za a yarda da hakan ne, idan aka yi la’akari da kusan duk kauyukan da ke nan an kawo musu hari.”