‘Iyayen yaran da ake wa fyade ba su ba mu hadin kai – Barista Huwaila Ibrahim
Tarihin rayuwa: Sunana Barista Huwaila Ibrahim Muhammad, an haife ni a Kano. Mahaifina dan kasuwa ne kuma ya rasu tun muna kanana. Mahaifiyarmu malamar jami’a ce Farfesa Gaji Fatima dantata, ta rike mu ni da kannena hudu har muka girma muka yi karatu. Na yi karatun firamare a Legas, bayan mahaifunmu ya rasu muka dawo […]
Tarihin rayuwa:
Sunana Barista Huwaila Ibrahim Muhammad, an haife ni a Kano. Mahaifina dan kasuwa ne kuma ya rasu tun muna kanana. Mahaifiyarmu malamar jami’a ce Farfesa Gaji Fatima dantata, ta rike mu ni da kannena hudu har muka girma muka yi karatu. Na yi karatun firamare a Legas, bayan mahaifunmu ya rasu muka dawo Kano inda na ci gaba da karatuna a nan. Na yi kuma sakandarena a Makarantar ’Yanmata ta Jogana. Bayan na kammala sai na tafi Kwalejin Share Fagen shiga Jami’a (CARS). Sannan na shiga Jami’ar Bayero da ke Kano, inda na karanta bangaren dokokin shari’a. Alhamdulillah na gama a shekarar 2000. A shekarar 2001 na je Makarantar Lauyoyi na yi jarrabawar kwarewa na ci. Sannan na je na yi hidimar kasa (NYSC) a shekarar 2003. Bayan na gama hidimar kasa sai na fara aiki inda na hadu da wani lauya a Kano muka rika zuwa kotu da shi don ganin yadda ake yin aiki har daga baya na zo na koya.
Sannan kuma na yi aiki a wani wuri shi ma a Kano ne. Daga baya sai na koma Jami’ar Bayero domin yin digiri na biyu. A daidai wannan lokacin BUK ta fara yin digiri na biyu wanda ba na malamai ba. Bayan na gama da yake ni mai son karatu ce sai na ga wani kws da ake yi a Cibiyar Fadada Nazarin Shari’a ta Jami’ar Legas. To daga nan sai na fara tunanin ni ma in fara wani aiki nawa, inda muka hadu da kawata abokiyar aikina kuma ’yar uwata A’isha Ado Abdullahi, da Sagir Gezawa da Abubakar Isah wadanda duk tare muka yi karatu a Jami’ar Bayero, sai dai ina dan gaba da su kadan. Sai muka hadu da babanmu Farfesa Tabi’u muka bude wata kungiya ta bayar da shawara wato Consultancy a shekarar 2005, saboda mu ma ’yan Arewa mu samu namu; domin za ki ga duk yawancin cibiyoyin bayar da shawarar kwarewa na ’yan Kudu ne.
Ayyukanta:
A ofishimu muna yin duk aikace-aikace irin na lauyoyi da suka hada da rubuta doka da bibiyar doka da duk wani abu da ya shafi doka. Sannan ba haka muka tsaya ba, muna yin bincike da ya shafi harkar shari’a. Muna bayar da horo kan yin sulhu. Sannan akwai kungiyoyi da nake ciki kamar kungiyar Lauyoyi ta kasa (NBA), da kungiyar Mata Lauyoyi ta kasa (FIDA). Abin da muka fi mai da hankali shi ne duk wani abu da ya danganci kare hakkokin yara da mata. Muna bin shari’o’in yin fyade da wulakanta mata da sauran wadannan abubuwa. Idan an kawo mana korafi za mu zauna mu duba mu sa a kira mijin matar shi ma mu ji daga gare shi. Idan muka ji mu ba da shawarwari a kai kafin a je kotu, idan kika ji an je kotu musamman a kan matsalar raba aure to abu ne ya turje, cin zali da cin zarafin ya yi yawa. Amma duk abin da aka ce babu gaskiya a ciki ba na so in alakanta kaina a ciki saboda tarbiyyar da aka dora ni a kanta. Ni a ra’ayina ko namiji ne na ga ana kokariin cin zarafinsa zan yi kokari in ga na tsaya masa, kamar matsalar da ta faru da Yunusa Yellow.
Sannan akwai wani bangare daga British Council (NSRP) da suka kafa suna yin ayyuka da yawa a Najeriya, sannan akwai wani kwamiti da suka kafa shekara hudu da suka wuce ni nake shugabancin kwamitin. Shi ma muna yin abubuwa na kare hakkin mata da yara. Sai dai abin da muka fi yi shi ne tattara shari’o’in, muna ganin adadin abin da aka samu na matsalolin cin zarafin mata da yara sannan za mu ga shari’u nawa aka iya magancewa, kuma nawa ne suke kotu, to irin wadannan duk kungiyar ke yi wanda ni ce nake shugabantar kungiyar.
Abin da ya sa matsalolin fyade ke karuwa:
Zan iya cewa ba karuwa suke ba, saboda fadakarwa da ake yi ga al’umma shi ya sa yanzu suke fitowa suke magantuwa. Da can idan kika duba ana yi, inda yanzu na kananan yara ne ya ta’azzzara. Akwai bangaren kula da wadannan matsaloli da aka bude kuma na ga suna yin aiki sosai. Sannan a nan Kano akwai wani bangare da aka bude na musamman na ’yan sanda domin kula da batun fyade, in dai ka je wannan wajen babu yadda za a yi ka ce ba a dauki wani mataki ba. Yawancin matsalolin da ake samu wajen kafa hujjoji da shaidu game da cewa an yi fyade gabatar da irin wadannan shaidu ke daukar lokaci.
Abin da ke faruwa shi ne idan aka kama mutum da zargin aikata fyade ita mahaifiyar yarinya da ta fara dubawa ta gani to a haka za ta dauke ta ta kai ta wajan ’yan sanda, su kuma daga nan za su dauke ku su kai ku asibiti a binciki yarinya a yi komai. Sannan asibiti za su rubuta rahoto su kai wa ’yan sanda domin ci gaba da bincike, idan suka yi bincike dangane da rahoton da suka samu daga asibiti wanda in laifin fyade ne za a caji mutum da laifin fyade. To in laifin fyade ne ba a ba da beli kuma duk wanda aka caja da laifin fyade za ki gan su a kurkuku ba za su fito ba sai idan an gama shari’ar.
kalubalen da ake fuskanta a shari’un fyade:
Kuma irin yadda mutanen unguwa suke taruwa a kan iyayen yarinyar da aka yi wa fyade su ba su hakuri, sai ki ga an yi fyade kiri-kiri an kuma cuci yarinya har karshen rayuwarta, amma an taru an danne iyayen yarinyar sun kasa karbar mata ’yanci. Yanzu duk shari’ar da za a yi ta fyade wallahi sai iyayen yarinya sun ba ka wahala, sai su ki ba ka hadin kai, sai ka yi ta lallaba su sannan za su yarda. Sai mun yi nisa a shari’a sannan ’yan unguwa za su zo wa iyaye a kan su janye. Kodayake yanzu mun fara samun sauki, domin yanzu duk wanda ya zo muna gaya masa cewa duk wanda ya kawo kara babu maganar janyewa tunda hukuma tana da hakki haka nan gwamnati, to dole sai an karba wa yarinya hakkinta.
Nasarorin da na samu:
Wai! Alhamdulillah zan iya cewa nasarori akwai su tunda na zama kwararriyar lauya (BAR) shekara 15 da suka wuce. Kuma na tsaya kan matsalolin mutane da yawa na karba musu ’yancinsu kamar matsalolin fyade ban san adadinsu ba, amma dai gaskiya ba zan ce na ci nasara ba domin a yanzu ba zan sa sunana a jerin manyan lauyoyi ba.
Mutane abin koyi:
Babbar wacce ta fi birge ni a rayuwa ita ce mahaifiyata saboda irin gwagwarmaya da ta yi a rayuwarta. Kin ga sai da ta haife mu mu biyar, sannan bayan mahaifinmu ya rasu ta koma makaranta ta yi digiri, ta kuma yi digiri na biyu da na uku, har ga shi a yanzu ta zama Farfesa. Alhamdulillah tana yin abinta cikin tsari ta kuma yi mana tarbiyya.
Abin da nake so a tuna ni da shi:
Abin da nake son bari a rayuwata shi ne in na mutu wata rana a rika tunawa da Barista Huwaila kan ta tsaya wajen kare hakkin marayu ta kwatarw a mata hakkinsu da duk wanda aka zalunta, to ina so a danganta ni da wadannan suffofi. Sannan ina so a tuna ni a kan wayar wa mutane kai musamamn a yanzu da na mayar da hankali a kan abubuwan da suka shafi yaki da shan miyagun kwayoyi. Ina so mu hadu mu kafa wani abu mai karfi wanda za mu tabbatar an samu zaman lafiya, samarinmu kowa ya samu abin yi ba wanda yake shan kwaya.
Shawararta ga mata:
Babbar shawarar da zan ba mata ita ce su san kansu su san Allah Ya ba su daraja da kima, su kuma kula da kansu. Mace ba a santa da raki da korafi ba. Mace ita uwa ce a gida idan ki ka zauna ki ka kama kanki za ki ga komai ya zo miki da sauki. Mace ta samu abin yi, ba mace ta tsaya ta zura ido sai ta jira an ba ta ba. Sannan mata su nemi ilimi domin duk wacce kika ga ta taka wani matsayi to ilimi ne ya kai ta. Iyaye su dage wajen sanya ido a kan ’ya’yansu domin yawancin fyade da ake yi sakacin iyaye ne da rashin kula suke janyowa. Za ki ga yarinya ta tafi makaranta a makare a matsayinki na uwa kin san adadin mintunan da za su dauke ta daga makarantarsu zuwa gidansu amma idan ta dawo a makare ba za a tambayi ina ta tsaya ba shi ke nan maganar ta wuce. Wannan ba daidai ba ne.