Iyayen yaron da ya rasu a gidan kangararrun yara na neman hakkinsu
Iyayen wani yaro mai suna Abubakar Idris da ya rasu sakamakon tsare shi a gidan kangararrun yara na Gwauron Dutse da ke Kano sun yi zargin cewa yaron ya mutu ne sakamkon azabtar da shi da ma’aikatan gidan suka yi, inda suka bukaci a bi musu hakkin dansu.Abubakar Idris ya rasu ne sakamkon ciwon kirji […]
Iyayen wani yaro mai suna Abubakar Idris da ya rasu sakamakon tsare shi a gidan kangararrun yara na Gwauron Dutse da ke Kano sun yi zargin cewa yaron ya mutu ne sakamkon azabtar da shi da ma’aikatan gidan suka yi, inda suka bukaci a bi musu hakkin dansu.
Abubakar Idris ya rasu ne sakamkon ciwon kirji da kafa da ya yi fama da shi na kwanaki a lokacin da yake zaman jiran shari’a a gidan kangararrun yaran.
Alkalin Kotun Shari’ar Musulunci ta Sabon Gari ’Yan Alluna ne ya ba da umarnin a tsare marigayi Abubakar Idris da kanensa Abdullahi Ali bayan da aka zarge su da yi wa wani yaro mai suna Jamilu rauni a Unguwar Gayawa kan sabani game da shiga wani sabon kulob din wasan kwallon kafa.
Rigimar a tsakanin Abdullahi da Jamilu, an ce sun soki juna da kibiya da almakashi. Sai dai raunin da Jamilu ya samu ya yi tsanani inda iyayensa suka yi karar marigayin da kanensa Abdullahi ga ’yan sanda kuma a ranar 27 ga Agusta aka gurfanar da su gaban kotun.
Alkalin Kotun Abubakar Mahmud Ayagi ya sa an tsare yaran a gidan kangararrun yara na Gwauron Dutse tare da dage shari’ar zuwa ranar 11 ga Agusta. Kuma Aminiya ta gano cewa kwanan yaran biyu a Gwauron Dutse aka bayar da belinsu. Sai dai da aka koma kotun a ranar 11 ga Agusta, Alkalin ya sake mayar da yaran Gwauron Dutse inda kwanansu shida da komawa Abubakar ya rasu.
Mahaifin marigayin Malam Idris Mohammad ya ce dansa ba ya da tarihin wani ciwo, kuma lafiya kalau aka tafi da shi Gwauron Dutse, amma sai gawarsa aka kawo masa.
Ya ce “Na ba mahaifin yaron da aka yi wa raunin hakuri, a ofishin ’yan sanda amma bai hakura ba. Kuma da Alkali ya tura su gidan kangararrun yara da kwana biyu wani surukinmu mai suna Muhammad ya yi belinsu a kan Naira dubu bakwai suka dawo gida. Amma da muka koma kotu ranar 11 ga Agusta, sai Alkalin ya soke belin ya mayar da su Gwauron Dutse na mako biyu.” Ya ce “Kwanansu shida a ranar 17 ga Agusta aka kawo min gawar dana ba tare da an sanar da ni labarin rashin lafiyarsa ba.”
kanen marigayin Abdullahi Ali ya bayyana wa Aminiya cewa “Bayan Alkalin ya sake mayar da mu Gwauron Dutse, wani ma’aikacin gidan mai suna Malam Isah ya shiga zaginmu cewa ba ma jin magana ga shi bayan mun fita mun sake yin wani laifi an sake dawo da mu. Sai muka ce a kan laifin farko aka dawo da mu, amma bai yarda ba. Sai ya bayar da umarnin a raba mana daki ya ce a kai ni dakin manya, yayana a kai shi dakin yara, sai marigayin ya ce ai shi ne babba. Wannan magana ita ta fusata Malam Isah ya sa marigayin tsallen kwado. Daga lokacin ba mu sake haduwa da marigayin ba sai a ranar Juma’a da muka fito Sallah, ya gaya min cewa tunda ya yi tsallen kwadon nan ya ji zuciyarsa ta amsa ga kuma ciwon kirji da kafa da yake fama da su.”
Abdullahi ya ce daga baya wani yaro da suke daki daya da Abubakar ya gaya masa cewa tunda ya koma dakin yake cikin ciwo ba ya ko iya zuwa ban-daki. Da ya yi kwana shida a wannan hali sai aka kai shi kotu inda Alkalin ya bayar da kudi aka kai shi asibiti kuma ya rasu a ranar. “Ina tsare aka zo aka tafi da ni in raka su gidanmu saboda sun yi yawon neman gidan sun rasa. Da muka kai gawar gidan sai aka sake dawo da ni Gwauron Dutse sai washegari aka zo aka tafi da ni,” inji shi.
Kakakin Ma’aikatar Mata da Walwalar Jama’a, Malam Sanusi Abdullahi kofar Na’isa ya tabbatar da rasuwar Abubakar a hannunsu, sai dai ya ce binciken da suka gudanar sun gano cewa ba a azabtar da yaron ba, kuma da ma ba ya da lafiya.