Izala ta bude kamfanin jigilar matafiya ta jiragen sama
kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’ikamatis Sunnah ta kasa reshen Jihar Filato ta bude kamfanin jigilar matafiya ta jiragen sama zuwa kasashe daban-daban na duniya. Shugaban majalisar malamai na kungiyar, reshen Jihar Filato Dakta Hassan Abubakar Dikko ne ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi a wajen wani taron wa’azi tare da kaddamar da gidauniyar […]
kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’ikamatis Sunnah ta kasa reshen Jihar Filato ta bude kamfanin jigilar matafiya ta jiragen sama zuwa kasashe daban-daban na duniya.
Shugaban majalisar malamai na kungiyar, reshen Jihar Filato Dakta Hassan Abubakar Dikko ne ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi a wajen wani taron wa’azi tare da kaddamar da gidauniyar neman gudunmawa da kungiyar ta shirya a garin Jos a karshen makon da ya gabata.
Ya ce “Tuni mun samu lasisin bude wannan kamfani, tare da cika dukkan ka’idojin da suka kamata da kuma bude ofisoshin wannan kamfani a garin Jos da Abuja.”
Ya ce sun yi taro a Saudiyya da Ingila duk a kan bude wannan kamfani.
Ya yi bayanin cewa wannan kamfani zai rika daukar masu umara zuwa kasa mai tsarki tare da daukar matafiya zuwa kasashen Larabawa da sauran kasashen duniya.
Ya ce “Ganin irin muhimmancin da wannan harka ta jigilar matafiya ta jiragen sama take da shi, ya sanya kungiyar reshen Jihar Filato ta bude wannan kamfani.”