Izala ta bude rediyo da talabijin
Taimakon da kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah take karba daga masallatai sama da dubu 15 a kaskashin gidauniyar MANARA, ya taimaka wajen kula da marayu da samar da kayan masarufi ga wasu daga cikin wadanda matsalar tashe- tashen hankula a jihohin Arewa maso Gabas ta shafa. Shugaban kungiyar na kasa Sheikh Abdullahi Bala […]
Taimakon da kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah take karba daga masallatai sama da dubu 15 a kaskashin gidauniyar MANARA, ya taimaka wajen kula da marayu da samar da kayan masarufi ga wasu daga cikin wadanda matsalar tashe- tashen hankula a jihohin Arewa maso Gabas ta shafa.
Shugaban kungiyar na kasa Sheikh Abdullahi Bala Lau ne ya bayyana hakan a yayin kaddamar tashar talabijin da rediyo na MANARA da kungiyar ta kafa a shekaranjiya Laraba a Abuja.
Sheikh Bala Lau ya ce taimakon wanda a ke bada shi ta hanyar sayen kati, sannan a samu sakon abin da ke cikin asusunsa da inda ya zo ta hanyar amfani da na’ura ne ya ba kungiyar damar kafa tashar rediyo da talabijin ta duniya mai suna Manara da za a iya kama ta a yankunan Afirka da Asiya inda zai rika yada shirye-shiryen da suka shafi addinin Musulunci kai-tsaye.
Sheikh Bala Lau ya ce kodayake Najeriya ba ta hana al’ummarta kama tashoshin talabijin na kowane irin nau’i ba daga kasashen waje ciki har da na fitsara, dokokinta sun hana kafa tashar yada addini daga cikin kasarta, saboda haka za su rika tsara shirye-shiryen ne a nan Najeriya, su aika da su waje inda za a rika watso shi zuwa nan Najeriya da sauran kasashen Afirka da Asiya ta hanyar amfani da kumbon Nile daga abokan huldarsu na waje.
Mai Alfarma Sarkin Musulmi wanda Andoma na Doma Alhaji Ahmad Aliyu Oga ya wakilta, ya bukaci kungiyar Izala ta yi amfani da tashoshin rediyo da talabijin na Manara wajen ilimantar da al’umma su rika gudanar da al’amuransu ta hanyar lumana wanda ya ce shi ne hakikanin karantarwar Manzon Allah (SAW).
Sarkin Musulmi ya yi Allah wadai da tashe-tashen hankula da suka yawaita a duniya da yawanci suke faruwa a kasashen Musulmi. Gwamnan Jihar Zamfara Alhaji Abdul’aziz Yari Abubakar wanda shi ne babban bako mai jawabi, ya bukaci mawadata da cibiyoyin gwamnati da masu zaman kansu, su taimaka wajen dorewar kafofin biyu, ta hanyar daukan nauyin wasu daga cikin shirye-shiryensu. Wasu bankuna da kamfanoni da kuma cibiyoyin gwamnati da suka aike da sakon fatan alheri ga kungiyar, sun bayyana sha’awarsu na kulla alakar arziki da kafofin biyu.