Izala ta bukaci gwamnatin Buhari ta kara wa Farfesa Jega wa’adi

kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa ta bukaci gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta kara wa Shugaban Hukumar Zabe ta kasa (INEC) Farfesa Attahiru Jega wani wa’adi domin ya ci gaba da shugabancin hukumar.  Shugaban Majalisar Malamai ta kungiyar ta kasa, Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ne, ya bukaci a lokacin da […]

Izala ta bukaci gwamnatin Buhari ta kara wa Farfesa Jega wa’adi
Izala ta bukaci gwamnatin Buhari ta kara wa Farfesa Jega wa’adi

kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa ta bukaci gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta kara wa Shugaban Hukumar Zabe ta kasa (INEC) Farfesa Attahiru Jega wani wa’adi domin ya ci gaba da shugabancin hukumar. 

Shugaban Majalisar Malamai ta kungiyar ta kasa, Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ne, ya bukaci a lokacin da yake jawabi a wajen rufe taron bita na kasa karo na 22 da kungiyar ta shirya a garin Jos.
Ya ce, “Muna rokon gwamnatin Buhari ta kara wa Farfesa Attahiru Jega lokaci kan shugabancin Hukumar Zabe ta kasa don ya kammala aikin yadda za a rika gudanar da zabubbuka masu kyau a kasar nan. Mun gamsu da irin aikin da Farfesa Jega ya gudanar a lokacin zabubbukan da suka gabata, kuma ba ma son a sake yin wuru-wuru a zabubbukan Najeriya. Don haka a kara wa Jega lokaci domin ya ci gaba da jagorancin wannan hukuma, har zuwa lokacin zabubbuka na gaba.”
Sheikh Jingir kuma ya roki Farfesa Attahiru Jega cewa idan aka kara masa lokaci, ya yi hakuri ya taimaka ya ci gaba da rike shugabancin Hukumar INEC. Ya ce “Kada ka dubi wahalar da ka sha a lokacin zabubbukan da aka gudanar a Najeriya, ka taimaka ka ci gaba da jagorancin hukumar domin ka dada ba da gudunmawarka wajen gyara wannan kasa.”
Ya yaba wa hukumar zaben kan yadda ta yi amfani da na’urar tantance masu zabe, inda ya ce na’urar ta taimaka wajen samun nasarar zaben da aka gudanar a kasar nan. Don haka ya yi kira a ci gaba da amfani da na’urar a zabubbuka nag aba.
Sheikh Jingir ya yi kira ga gwamnatin Buhari da kada ta nada mutanen da ba su cancanta ba a cikinta, ya ce ya kamata duk wanda aka nada shi a cikin gwamnatin ya rike amana.
Taron bitar na bana mai taken: “Kyakkyawan jagoranci shi ne daukakar al’umma da ci gabanta,” manyan malamai ne suka gabatar da makaloli daban-daban wadanda suka hada da “Tasirin adalci ga jagoranci” da Sheikh Sani Yahya Jingir ya gabatar. Sai “Gaskiya da rikon amana a fuskar mu’amala,” da Sheikh Yusuf Sambo Rigachikun ya gabatar. Sai “Istikama” da Sheikh Sa’idu Hassan Jingir ya gabatar.
Sauran su ne “Matakan ba da ilimi ingantatce,” da Dokta Yusuf Abdullahi ya gabatar da kuma “Hadarin Shi’a ga al’ummar Musulmi” da Dokta Bashir Imam ya gabatar.