Izala ta bukaci jama’a su yi zabe cikin lumana
kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa ta bukaci al’ummar kasar nan, su gudanar da harkokin siyasa tare da yin zabe cikin lumana, inda ta ce ba ta da jam’iyya amma ’ya’yanta su jefa wa duk mutumin kirki kuri’arsu. Shugaban Majalisar Malamai ta kungiyar ta kasa reshen Sheikh Sani Yahaya Jingir ne ya […]
kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa ta bukaci al’ummar kasar nan, su gudanar da harkokin siyasa tare da yin zabe cikin lumana, inda ta ce ba ta da jam’iyya amma ’ya’yanta su jefa wa duk mutumin kirki kuri’arsu.
Shugaban Majalisar Malamai ta kungiyar ta kasa reshen Sheikh Sani Yahaya Jingir ne ya bayyana haka a wa’azin kasa da kungiyar ta gudanar a Abuja a karshen makon jiya.
Sheikh Sani Yahaya Jingir ya yi kira a tunkari zaben cikin lumana. Ya ce addinin Musulunci rayuwa ce gaba daya ciki kuma har da siyasa. Kowa ya je ya yi zabe domin Allah, ba domin kwadayin abin duniya ba. “Jama’a su lura da cancanta da yadda za a maido da tsaro a kasar nan da ci gaban bunkasar ilimi da tattalin arziki,” inji shi.
Ya ce duk wadannan ba za su yiwu ba, sai an lura da cancanta, ya ce duk wani dan siyasa da ya fito takara a duba tarihinsa, kada a yi wasa da kuri’a.
Ya yaba wa Hukumar INEC da tace ta shirya gudanar da zaben domin a wannan karo adadin wadanda suka yi rajista sun fi wadanda suka yi zabe a shekarar 2011.
Shugaban ya yi kira kada kowa ya bari a zolaye shi ya yi fada, ya ce gyara a ke bukata ba fada ba.