Izala ta goyi bayan gwamnatin Buhari kan yaki da cin hanci

kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa ta nuna goyon bayanta ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari, kan shirin gwamnatinsa na yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya.  Shugaban Majalisar Malamai ta kungiyar ta kasa Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ne ya bayyana haka, a lokacin da yake jawabi a wajen rufe taron […]

Izala ta goyi bayan gwamnatin Buhari kan yaki da cin hanci
Izala ta goyi bayan gwamnatin Buhari kan yaki da cin hanci

kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa ta nuna goyon bayanta ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari, kan shirin gwamnatinsa na yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya.  Shugaban Majalisar Malamai ta kungiyar ta kasa Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ne ya bayyana haka, a lokacin da yake jawabi a wajen rufe taron kara wa juna sani na kasa na kungiyar karo 20, mai taken: “Yaki da Cin hanci da Rashawa a Addinin Musulunci,” da kungiyar ta shirya a garin Jos.
Sheikh Sani Yahaya Jingir ya ce babu shakka cin hanci da rashawa ne babbar matsalar da take damun Najeriya. “Don haka muna goyon bayan Shugaban kasa Muhammadu Buhari kan shirinsa na yaki da cin hanci da rashawa kuma muna rokon Allah Ya taimake shi, kan wannan babban aiki da ya sanya a gaba,” inji shi.
Ya kara da cewa: “A gwamnatin da ta gabata an kashe dubban mutane a Najeriya sakamakon rikice-rikice. Amma daga lokacin da gwamnatin Shugaba Buhari ta hau gadon mulkin Najeriya, zuwa yanzu mutum zai je duk inda yake so ya je a Najeriya ba tare da wata fargaba ko tsoro ba, saboda zaman lafiyar da aka samu.  Don haka muna yaba wa gwamnatin Buhari da jami’anta, kan wannan gagarumar nasara da ta samu na samar da tsaro a kasar nan.”
Ya yi kira ga al’ummar kasar nan su zauna lafiya da junansu. Ya ce “Allah ne Ya hada mu a kasar nan, don haka mu zauna lafiya kada Musulmi ya cuci wanda ba Musulmi ba, kada kuma wanda ba Musulmi ba, ya cuci Musulmi.”
A jawabin tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Babayo Garba Gamawa ya ce babu shakka wannan taron kara wa juna sani zai kara wa jama’a sanin illolin cin hanci da rashawa, inda ya ce cin hanci da rashawa suna zuwa a fannoni daban-daban. Kuma idan jama’a suka yi kokari suka yi aiki da abubuwan da malamai suke koyarwa za a magance matsalar.
Ya yi  kira ga malamai su rika shiga  harkokin siyasa, domin idan wadanda suka san Allah suka karbi jagoranci za a samu gyara a kasar nan.
Tun da farko a jawabin Shugaban Shirya Taron kara wa Juna Sani na kasa na kungiyar Hafiz Aminu Yusuf Nuhu ya ce taron karo  na 20 da aka yi kwana uku ana gudanarwa, an samu mahalarta 883 da suka fito daga jihohi 29 na Najeriya da Jamhuriyar Nijar.
Ya ce manyan malamai sun gabatar da makaloli da suka hada da Sheikh Sani Yahya Jingir wanda ya gabatar da makala mai taken: “Ci gaban Izala a yau.” Sai Mataimakinsa Sheikh Yusuf Muhammad Sambo Rigachikum ya gabatar da makala mai taken: “Siffofi da dabi’un Mai Wa’azi.” Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya gabatar da makala mai taken: “Sharrin Shi’a da Makirce-Makircensu.” Sai Shugaban
kungiyar ta kasa Sheikh Abdul-Nasir Abdul-Muhyi ya gabatar da makala mai taken: “Aikin Hajji da Hukunce-Hukuncensa.” Da sauran malamai da suka gabatar da makaloli a fannoni da dama.

Zazzaɓin Lassa ya kashe mutum 214 a Najeriya — NCDC

An kama masu garkuwa da mutane a Borno 

Rikicin ya kunno kai a Hukumar Alhazan Jihar Delta

Sojoji sun ceto mutane 5 da ISWAP ta sace a Harin Ngoshe