Izala ta kaddamar da gidauniyar neman tallafin ayyukan shekara a Abuja

An yi kira ga al’ummar Musulmi su kara himma wajen bayar da taimako don ayyukan raya addinin ta fuskoki daban-daban, musamman a lokacin azumin watan Ramadan da ke tafe. Kiran ya fito ne daga manyan shugabannin addini da na gwamnati da suka halarci taron kaddamar da gidauniyar neman tallafin Naira miliyan 500 domin ayyukan shekarar […]

Izala ta kaddamar da gidauniyar neman tallafin ayyukan shekara a Abuja

Na biyu daga hagu, Shugaban Majalisar Malamai ta Kungiyar Izala ta Abuja Ustaz Ibrahim Muhammad Duguri; a dama wakilin Sarkin Bwari, Barden Bwari Kyaftin Aliyu Garba lokacin kaddamar da neman taimako na kungiyar Izala

An yi kira ga al’ummar Musulmi su kara himma wajen bayar da taimako don ayyukan raya addinin ta fuskoki daban-daban, musamman a lokacin azumin watan Ramadan da ke tafe.

Kiran ya fito ne daga manyan shugabannin addini da na gwamnati da suka halarci taron kaddamar da gidauniyar neman tallafin Naira miliyan 500 domin ayyukan shekarar nan da kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah (JIBWIS), reshen Abuja ta gudanar a Babban Masallacin Kasa da ke Abuja.

Shugaban Majalisar Malamai ta Kungiyar reshen Abuja, Ustaz Ibrahim Muhammad Duguri, ya ce bisa al’ada kowace shekara kungiyar daga matakan rassa zuwa kasa tana gudanar da ayyukan addini kamar tura malamai zuwa kananan hukumomin Abuja guda shida da kuma wasu yankuna na musamman domin tafsirin Alkur’ani a lokacin Ramadan da ke tafe da ma sauran ayyukan addini.

Ya ce akwai gwaggwabar lada da ke tattare da bayar da taimakon ga addini kasancewar Allah zai daukaka wanda ya bayar tun daga nan duniya har zuwa ranar Kiyama.  Ya ce abin da mutum ya bayar shi ne nasa; kuma abin da mutum ya rike to ba na sa ba ne, na magada ne. Domin haka, akwai bukatar Musulmi ba wai sai masu hannu da shuni ba, duk karancin arzikin mutum da shi zai taimaka, domin Allah Zai ninninka Ya yalwata tare da kuma yaukaka arzikin wanda yake ciyar da dukiyarsa a hanyar Allah.

Ustaz Ibrahim Duguri ya ce kungiyar ta himmatu wajen yin amfani da kudin da aka tara domin ayyukan da aka tara su dominsu, kuma jama’a za su shaida ayyukan da za a yi da kudaden da suka bayar, sa’annan ya ce har yanzu kofa a bude take ga dukkan mai son bayar da tallafi.

Mai martaba Sarkin Bwari, wanda Kyaftin Aliyu Garba, Barden Bwari ya wakilta, ya yi kira ga shugabannin addini su tashi tsaye wajen fantsama cikin yankunan karkara domin yada addinin Musulunci. Ya ce yanzu ilimi ya wadatu a birane, amma  ana matukar yunwarsa a karkara.  Ya ce akwai mutane da dama a lungu da sako-sako da suke neman shiga addinin Musuluncin; don haka suna bukatar a tallata musu tare da wayar musu da kai game da addinin.

Aminiya ta fahimci cewa, baya ga gudanar da tafsirin Ramadan, kungiyar tana neman wadannan kudade ne domin sayen motoci uku domin aikin Da’awah da gina makarantun Islamiyya a Birnin Tarayya da bayar da taiamko lokacin ayyukan lokacin Hajji da kwaskwarimar Sakatariyar kungiyar a Abuja da tarurrukan kara wa juna sani.

An dai tara kudi fiye da miliyan uku a yayin kaddamarwar.