Izala ta kaddamar da shirin samar da kafafun roba ga kasassu

kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kaddamar da shirinta na samar da kafafu da hannuwan roba ga nakasassu inda aka tsara taimaka wa mutum 2,500 a fadin kasar nan. Shirin wanda zai gudana rukuni-rukuni kamar yadda shugaban Gidauniyar MANARA da ke jagorantar aikin Malam Abdullahi Abdulmalik Diggi ya bayyana, zai fara ne da […]

Izala ta kaddamar da shirin samar da kafafun roba ga kasassu
Izala ta kaddamar da shirin samar da kafafun roba ga kasassu

kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kaddamar da shirinta na samar da kafafu da hannuwan roba ga nakasassu inda aka tsara taimaka wa mutum 2,500 a fadin kasar nan.
Shirin wanda zai gudana rukuni-rukuni kamar yadda shugaban Gidauniyar MANARA da ke jagorantar aikin Malam Abdullahi Abdulmalik Diggi ya bayyana, zai fara ne da jihohin Sakkwato da Benuwai da Yobe da Neja da kuma Abuja a karon farko wanda aka fara a shekaranjiya Laraba a Abuja zuwa yau Juma’a.
Malam Abdullahi Diggi wanda ya wakilci shugaban kungiyar na kasa Sheikh Abdllahi Bala Lau a wajen taron, ya ce tallafin na hadin gwiwa ne a tsakanin Gidauniyar MANARA da wata takwararta ta kasar Indiya. Ya ce da farko za a gwada mahalarta aikin ne a hannu ko kafar da ta samu nakasa, daga bisani a samar da madadin na roba a cikin wata biyu, daidai da girma ko tsawon mai nakasar.
A zantawarsa da Aminiya wani da ya amfana da shirin mai suna Abubakar danjuma daga karamar Hukumar Chanchaga a Jihar Neja, bayyana jin dadinsa ya yi tare da fatan alheri ga kungiyar.