Izala ta kai ziyarar kyautata dangantaka Gidan kadiriyya
A ranar Lahadi da ta gabata ne kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah reshen Jihar Kano a karkashin jagorancin Sheikh Abdullahi Saleh Pakistan da ’yan majalisar zartarwarsa da shugabannin kungiyar na kananan hukumomin jihar 44 suka kai wa Gidan kadiriyya ziyarar girmamawa.Tawagar ta samu tarbar Shugaban darikar kadiriyya ta Afirka ta Yamma, Sheikh karibullah […]
A ranar Lahadi da ta gabata ne kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah reshen Jihar Kano a karkashin jagorancin Sheikh Abdullahi Saleh Pakistan da ’yan majalisar zartarwarsa da shugabannin kungiyar na kananan hukumomin jihar 44 suka kai wa Gidan kadiriyya ziyarar girmamawa.
Tawagar ta samu tarbar Shugaban darikar kadiriyya ta Afirka ta Yamma, Sheikh karibullah Nasiru Kabara tare da manyan hadimansa.
A lokacin da yake gabatar da jawabi Dokta Abdullahi Saleh Pakistan, ya bayyana wannan ziyara a matsayin makamanciyar wacce magabatansu suka yi a sama da shekara 20 da suka gabata, inda marigayi Sheikh Nasiru Kabara ya yi tattaki zuwa Kaduna ya ziyarci marigayi Sheikh Abubakar Mahmud Gumi, daga baya shi ma ya ziyace shi.
Dokta Abdullahi Pakistan ya ce makasudin ziyarar shi ne “Domin sabunta ’yan uwantakar da ke tsakaninmu da kuma kara samun fahimta da sassauta harshe ga juna da samun cikakken hadin kai a kan koyarwar Alkur’ani da Hadisan Manzon (SAW) bisa fahimtar magabata, wato sahabbai da wadanda suka biyo bayansu,” inji shi.
Ya nuna damuwa kan rashin hadin kan Musulmi duk da irin kalubalen da suke fuskanta a wannan lokaci na zubar da jini da koma bayan kasuwanci da sauran al’amura.
Da yake maida jawabi, Khalifa Sheikh karibullah, ya bayyana farin cikinsa da wannan ziyara, inda ya yi wa Allah godiya da Ya nuna masa wannan rana da ta tunatar da shi makamanciyarta da ta faru ga magabatansa.
Ya yaba wannan yunkuri da Dokta Abdullahi Saleh Pakistan yake yi na sassauto da damuwa da kuma farfado da hadin kan Musulmi. Ya ce Musulmi ba za su yi kima da kwarjini ba har sai sun dunkule wuri guda.
Sheikh Karibullah ya gabatar da kyautar littattafai ga jagoran na Izala a matsayin tukwicin yaba wannan ziyara.
Daga cikin wadanda suka rufa wa Shugaban na Izala baya har da Shugaban Majalisar Dattawan kungiyar Sheikh Abdulwahhab Abdullah da Shugaban Kwamitin Yada Labarai na kasa na kungiyar, kuma kakakinta a jihar, Malam Ali dan Abba .