Izala ta shawarci jama’a su zabi cancanta ba jam’iyya ba
kungiyar Jama’atul Izalatil Bid’a Wa’ikamatis Sunnah ta shawarci jama’a su zabi cancanta ba a jam’iyya ba a zabe mai zuwa. Shugaban kungiyar na kasa Sheikh Abdullahi Bala Lau ya yi wannan kira a Sakatariyar kungiyar da ke birnin tarayya Abuja a ranar Litinin.Ya ce akwai bukatar nutsuwa tare da aiki da hankali wurin tantance wadanda […]
kungiyar Jama’atul Izalatil Bid’a Wa’ikamatis Sunnah ta shawarci jama’a su zabi cancanta ba a jam’iyya ba a zabe mai zuwa.
Shugaban kungiyar na kasa Sheikh Abdullahi Bala Lau ya yi wannan kira a Sakatariyar kungiyar da ke birnin tarayya Abuja a ranar Litinin.
Ya ce akwai bukatar nutsuwa tare da aiki da hankali wurin tantance wadanda suka kamata a zaba, wadanda za su yi tsayin daka domin kare hakkin mutanen da suke jagoranta.
Shugaban ya yi kira na musamman ga malaman addini su yi taka tsan-tsan wurin mu’amala da ’yan siyasa, su yi kokarin gaya musu gaskiya, kuma su wayar da kan mutane a kan muhimmancin zabe.
“Malamai su fahimtar da al’umma illar yin siyasa domin kudi, siyasar kudi sayar da ’yanci ne. Hadisi ya inganta daga Manzo Allah cewa duk wanda ya zabi shugaba ya yi masa mubaya’a saboda abin duniya, Allah ba zai yi masa kallon rahama a ranar alkiyama ba, saboda haka duk mai zabe ya zabi wanda zai tsare masa addininsa, jininsa, dukiyarsa, nasabarsa da kwakwalwarsa wato hankalinsa. Don haka lokaci ya wuce na yin siyasar kudi ko hargowa ko rashin mutunci, kowa halinsa ya fisshe shi.” Inji Shugaban.
Shehin Malamin ya kara da cewa, “Wani Taabi’ii ya ce: “Zamaninku shi ne mai mulkinku, idan mai mulkinku ya yi kyau sai zamaninku ya yi kyau, idan mai mulkinku ya lalace sai zamaninku ya lalace” Baihaki 17,095. Don haka akwai bukatar nutsuwa kwarai da gaske domin zaben mutane”
A karshe shugaban ya bukaci mutane su guji yada jita-jita, domin duk mutumin da ba shi da aiki sai kirkira da kuma yada karya, to tabbas yana tare da fushin Allah.