Izala ta shirya wa bita malaman da za suyi tafsirin bana bita a Gombe
Ganin azumin watan na ta karatowa, hakan tasa Kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta Kasa reshen Jihar Gombe ta shirya wa malaman da za su yi tafsirin watan azumin bana taron bita don fadarkar da su su shirya wa aikin da ke gabansu. Da yake jawabi, Shugaban Kwamitin Shirya Tafsirin na bana, Dokta […]
Waxansu daga cikin mahalarta taron
Ganin azumin watan na ta karatowa, hakan tasa Kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta Kasa reshen Jihar Gombe ta shirya wa malaman da za su yi tafsirin watan azumin bana taron bita don fadarkar da su su shirya wa aikin da ke gabansu.
Da yake jawabi, Shugaban Kwamitin Shirya Tafsirin na bana, Dokta Rasheed Abdul-ganiy na Jami’ar Jihar Gombe ya ce ya kamata mai tafsir ya san kalmomi da ma’anoninsu kafin ya gabatar da Tafsiri.
Dokta Rasheed Abdul-ganiy ya ce akwai aiki a gaban malaman tafsiri domin wadansu mutane imaninsu ya yi rauni, don haka sai malamai sun yi da gaske.
A jawabin, Babban Hakimin Birnin Gombe da Kewaye Alhaji Abdulkadir Abubakar, Yariman Gombe, ya jawo hankalin malamai ne kan su fadakar da al’umma sosai game yadda zinace-zinace da luwadi suka yi yawa a tsakanin jama’a.
Yariman Gombe wanda ya samu wakilcin Alhaji Yaya Hammari, ya kara da cewa a wasu jihohin ana fama da rikice-rikice, don haka ya bukaci a tashi tsaye da addu’a kan Allah Ya kawo karshen lamarin.
Shugaban Kungiyar Izala ta Jihar Gombe Alhaji Salisu Muhammad Gombe, ya ce duk mai tafsiri kamata ya yi ya zama kamar limamin Juma’a wajen karkata kan lamuran da suke faruwa yau da kullum a lokacin tafsirai.
Alhaji Salisu Gombe, ya kara da cewa idan annoba ta taso a mayar da hankali a kanta wajen isar da sako ga jama’a.
Sai ya hori mutane cewa su daina aibanta shugabani ko cin zarafinsu domin idan shugaba ya lalace mabiya ma za su lalace, “Kamata ya yi a ci gaba da yi musu addu’a,” inji shi.
A jawabin, Babban Bako na Musamman Dokta Isa Muhammad Wade, Kwamishinan Ilimi Mai Zurfi na Jihar Gombe, ya ce nauyi aka dora wa masu tafsirin wajen inganta rayuwar jama’a ta hanyar fada musu gaskiya.
Dokta Isa Wade, ya ce mafi yawan kasashen Musulmi a duniya suna fama da tashe-tashen hankula, don haka ya yi kira da a jajirce wajen yin addu’o’i musamman a lokacin azumi.
Daga nan sai ya yi kira cewa ganin azumi ya karato a rika wa’azuzzuka cikin hikima don dorewar zaman lafiya.