Izala ta taimaka wa marayu a Neja
kungiyar Jama’atu Izalatul Bidi’a Wa Ikamatus Sunnah reshen Jihar Neja ta taimaka wa marayu da marasa galihu fiye da 100 a Bida a matsayin daya daga cikin shirye-shiryen da ta bullo da shi na jinkan wadannan rukunan jama’a. Shugaban kungiyar Malam Haruna Musa wanda limamin masallacin Juma’a na Niteco Malam Idris Muhammad ya wakilta ne […]
kungiyar Jama’atu Izalatul Bidi’a Wa Ikamatus Sunnah reshen Jihar Neja ta taimaka wa marayu da marasa galihu fiye da 100 a Bida a matsayin daya daga cikin shirye-shiryen da ta bullo da shi na jinkan wadannan rukunan jama’a.
Shugaban kungiyar Malam Haruna Musa wanda limamin masallacin Juma’a na Niteco Malam Idris Muhammad ya wakilta ne ya jagoranci bayar da tallafin Naira dubu 10 ga wadanda suka samu cin moriyar shirin a fadar Mai Martaba Etsu Nupe Alhaji Yahaya Abubakar da ke Bidda.
Ya ce wadannan rukunin jama’ar an dade da yin watsi da su, kuma bai kamata a yi hakan ba.
Ya bayyana takaicinsa ganin yadda akasarin masu hannu da shuni ke sakaci wajen taimaka wa marayu da marasa galihu domin samun babban rabo, “don haka a rika taimaka wa jama’a musamman marayu da marasa galihu.”
Ya yaba wa jama’ar da suka sadaukar da dukiyoyinsu domin tabbatar da ayyukan addinin Musulunci sun kankama a fadin kasar nan.
Ya ce a kowane lokaci a bude kofar kungiyar take domin bayar da gudunmuwa wajen taimaka wa marasa galihu.
“Ina fata wadanda za su taimaka wa kungiyar su nemi jami’an gudanarwarta a masallatansu don taimakon ya shiga hannun da ya kamata.”
Alhaji Yahaya Abubakar ya shawarci Musulmi su rungumi akidar taimaka wa juna daga cikin dukiyarsu, “idan za a taimaka bai lallai sai an debi mutane masu yawa kafin a taimaka wa marayu ko marasa galihu ba.”
Ya jaddada cewa gudanar da irin wadannan ayyukan na wanzar da kara dankon zumunci a tsakanin mutane.
Mai Martaba Etsu Nupe kuma Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Neja, Alhaji Yahaya Abubakar ya nuna jin dadinsa game da wannan aikin, inda ya ce Musulunci na alfahari da aikata shi a ko’ina, domin an gudanar da shi a lokacin da wadanda aka taimakawa ba su yi tsammani ba.
Ya ce “Ayyukan da wannan kungiyar ke aikatawa sun zama abin alfahari da kuma koyi ga sauran jama’a.” Inji shi.
Ya nemi wadanda aka taimakawa su yi amfani da taimakon ta hanyar da za ta amfane su, musamman juya shi ta yadda zai kasance musu jarin da za su gudanar da kananan sana’o’in da za su zame musu hanyar samun arziki mai albarka, sannan su rika yi wa wadanda suka samar da wadannan kudin addu’o’i.
Malama A’isha Ibrahim na daya daga cikin wadanda suka cin moriyar wannan shirin, ta shaida wa Aminiya cewa “Ina zaune ne a gida suka zo suka yi mini tambayoyin da suka shafi marayun da nake rike da su, ba a dade ba sai aka sake zuwa wurina cewa ana nema na a fadar Mai Martaba Etsu Nupe. Zuwanmu ke da wuya aka yi ta ba kowa Naira dubu 10 a matsayin kudin tallafi. Allah Ya saka musu da alherinsa.”